< Ishaya 51 >

1 “Ku kasa kunne gare ni, ku da kuna neman adalci kuke kuma neman Ubangiji. Dubi dutse daga inda aka yanke ku da kuma mahaƙar duwatsu inda aka fafe ku;
Entendez-moi, vous qui poursuivez la justice, vous qui cherchez Yahweh; considérez le rocher d’où vous avez été taillés et la carrière d’où vous avez été tirés.
2 dubi Ibrahim, mahaifinku, da Saratu, wadda ta haife ku. Sa’ad da na kira shi kaɗai ne, na kuma albarkace shi na kuma mai da shi da yawa.
Considérez Abraham, votre père, et Sara qui vous a enfantés; car je l’appelai quand il était seul, et je l’ai béni et multiplié.
3 Tabbatacce Ubangiji zai ta’azantar da Sihiyona zai kuma duba da tausayi a kan dukan kufanta; zai sa hamadanta ta zama kamar Eden, ƙeƙasasshiyar ƙasarta kamar lambun Ubangiji. Za a sami farin ciki da murna a cikinta, godiya da ƙarar rerawa.
Car Yahweh a consolé Sion, et il a consolé toutes ses ruines. Il a fait de son désert un Eden, et de sa solitude un jardin de Yahweh; On y trouvera la joie et l’allégresse, les actions de grâces et le bruit des chants.
4 “Ku kasa kunne gare ni, mutanena; ku ji ni, al’ummata. Doka za tă fito daga gare ni; shari’ata za tă zama haske ga al’ummai.
Sois attentif à ma voix, ô mon peuple; ô ma nation, prête-moi l’oreille! Car la loi sortira de moi, et j’établirai mon commandement pour être la lumière des peuples.
5 Adalcina na zuwa da sauri, cetona yana a kan hanya, hannuna kuma zai kawo adalci ga al’ummai. Tsibirai za su dube ni su kuma jira da sa zuciya don hannuna.
Ma justice est proche, mon salut va paraître, et mon bras jugera les peuples; les îles espèrent en moi et se confient dans mon bras.
6 Ku daga idanunku zuwa sammai ku dubi duniya a ƙasa; sammai za su ɓace kamar hayaƙi, duniya za tă shuɗe kamar riga mazaunanta kuma su mutu kamar ƙudaje. Amma cetona zai dawwama har abada, adalcina ba zai taɓa kāsa ba.
Levez vos yeux vers le ciel, et abaissez vos regards sur la terre; car les cieux se dissiperont comme une fumée, et la terre tombera en lambeaux comme un vêtement, et ses habitants périront de même. Mais mon salut durera éternellement, et ma justice ne périra pas.
7 “Ku ji ni, ku da kuka san abin da yake daidai, ku mutanen da kuke da dokata a zukatanku. Kada ku ji tsoron ba’ar da mutane suke yi ko ku firgita saboda zargin da suke yi.
Entendez-moi, vous qui connaissez la justice, ô peuple qui as ma loi dans ton cœur: Ne craignez pas les injures des hommes, et ne vous effrayez pas de leurs outrages!
8 Gama asu za su cinye su kamar riga; tsutsotsi za su cinye su kamar ulu. Amma adalcina zai dawwama har abada, cetona har dukan zamanai.”
Car la teigne les dévorera comme un vêtement, et la gerce les rongera comme la laine. Mais ma justice subsistera à jamais, et mon salut jusqu’aux siècles des siècles.
9 Ka tashi, ka tashi! Ka yafa wa kanka ƙarfi, Ya hannun Ubangiji; ka farka, kamar a kwanakin da suka wuce, kamar a zamanai na dā. Ba kai ba ne wanda ya yayyanka Rahab gunduwa-gunduwa, wanda ya soki dodon ruwan nan?
Réveille-toi, réveille-toi, revêts-toi de force, bras de Yahweh! Réveille-toi comme aux jours anciens, comme aux âges d’autrefois. N’est-ce pas toi qui taillas en pièces Rahab, qui transperças le dragon?
10 Ba kai ba ne ka busar da teku, ka busar da ruwan zurfafa masu girma, wanda ya yi hanya a cikin zurfafan teku saboda fansassu su ƙetare?
N’est-ce pas toi qui desséchas la mer, les eaux du grand abîme; qui fis des profondeurs de la mer un chemin, pour faire passer les rachetés?
11 Waɗanda Ubangiji ya fansar za su dawo. Za su shiga Sihiyona da waƙoƙi; madawwamin farin ciki zai rufe kansu da rawani. Murna da farin ciki zai cika su, baƙin ciki da nishi zai ɓace.
Ainsi les rachetés de Yahweh reviendront; ils viendront dans Sion avec des cris de joie; une allégresse éternelle couronnera leur tête, la joie et l’allégresse les envahiront; la douleur et le gémissement s’enfuiront.
12 “Ni kaɗai ne na ta’azantar da ku. Wane ne ku da kuke tsoron mutane masu mutuwa,’ya’yan mutane waɗanda suke ciyawa ne kawai,
C’est moi, c’est moi qui vous console. Qui es-tu pour craindre un homme mortel, un fils d’homme qui passe comme l’herbe;
13 har da kuka manta da Ubangiji Mahaliccinku, wanda ya shimfiɗa sammai ya kuma kafa harsashen duniya, har kuna zama da tsoro kowace rana saboda fushin masu zalunci, waɗanda sun ƙudura sai sun hallaka? Gama ina fushin mai zalunci?
pour oublier Yahweh, ton Créateur, qui a étendu les cieux et fondé la terre, et pour trembler perpétuellement, tout le jour, devant la fureur du tyran, lorsqu’il se prépare à te détruire? Et où est-elle ta fureur du tyran?
14 Ba da daɗewa za a’yantar da’yan kurkuku; ba za su mutu a kurkuku ba, ba kuwa za su rasa abinci ba.
Bientôt celui qui est courbé sera délié; il ne mourra pas dans la fosse, et son pain ne lui manquera pas.
15 Gama ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya dama teku domin raƙumansa su yi ruri, Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.
Moi, je suis Yahweh, ton Dieu, qui soulève la mer, et ses flots mugissent; Yahweh des armées est son nom.
16 Na sa maganata a bakinka na kuma rufe ka da inuwar hannuna, Na shimfiɗa sammai, na kafa harsashen duniya, na kuma ce wa Sihiyona, ‘Ku mutanena ne.’”
J’ai mis mes paroles dans ta bouche, et je t’ai couvert de l’ombre de ma main, pour planter des cieux et fonder une terre, et pour dire à Sion: « Tu es mon peuple! »
17 Ki farka, ki farka! Ki tashi, ya Urushalima, ke da kika sha daga hannun Ubangiji kwaf na fushinsa, ke da kika shanye har ƙasar kwaf kwaf da ya sa mutane suna tangaɗi.
Réveille-toi, réveille-toi, lève-toi, Jérusalem, qui as bu de la main de Yahweh la coupe de sa colère, qui as bu, qui as vidé le calice d’étourdissement!
18 Cikin dukan’ya’yan da ta haifa; cikin dukan’ya’yan da ta yi reno babu wani da zai kama hannunta.
Pas un qui l’ait guidée, de tous les fils qu’elle avait enfantés. Pas un qui l’ait prise par la main, de tous les fils qu’elle avait élevés.
19 Waɗannan masifu riɓi biyu sun auko miki, wa zai ta’azantar da ke? Lalaci da hallaka, yunwa da takobi, wa zai ƙarfafa ki?
Ces deux malheurs t’ont frappée: — qui t’adressera des paroles de pitié? — La dévastation et la ruine, la famine et l’épée — comment te consolerai-je? —
20 ’Ya’yanki sun sume; sun kwanta kusurwar kowane titi, kamar barewar da aka kama da tarko. Sun cika da fushin Ubangiji da kuma tsawatawar Allahnki.
Tes fils, épuisés de force, sont gisants au coin de toutes les rues, comme une antilope dans le filet du chasseur, ivres de la fureur de Yahweh, de la menace de ton Dieu.
21 Saboda haka ki ji wannan, ke mai wahala, wadda ta bugu, amma ba da ruwan inabi.
C’est pourquoi, entends ceci, malheureuse, enivrée, mais non de vin!
22 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, Allahnki, wanda ya kāre mutanensa, “Duba, na ƙwace daga hannunki kwaf da ya sa ki tangaɗi; daga wannan kwaf, kwaf na fushina, ba za ki ƙara sha ba.
Ainsi parle ton Seigneur Yahweh, ton Dieu, qui défend son peuple: Voici que j’ai ôté de ta main la coupe d’étourdissement, le calice de ma colère; tu ne les boiras plus désormais.
23 Zan sa shi a hannuwan masu gwada miki azaba, waɗanda suke ce miki, ‘Fāɗi rubda ciki don mu iya taka a kanki.’ Kika kuma mai da bayanki kamar ƙasa, kamar titin da ake takawa a kai.”
Je les mettrai dans la main de tes persécuteurs, de ceux qui te disaient: « Courbe-toi, que nous passions! » Et tu faisais de ton dos comme un sol, comme une rue pour les passants!

< Ishaya 51 >