< Hosiya 7 >

1 a duka sa’ad da zan warkar da Isra’ila, zunuban Efraim za su tonu za a kuma bayyana laifofin Samariya. Suna ruɗu, ɓarayi sukan fasa su shiga gidaje,’yan fashi sukan yi fashi a tituna;
我想医治以色列的时候, 以法莲的罪孽和撒马利亚的罪恶就显露出来。 他们行事虚谎, 内有贼人入室偷窃, 外有强盗成群骚扰。
2 amma ba su gane cewa na tuna da dukan ayyukan muguntarsu ba. Zunubansu sun kewaye su; kullum suna a gabana.
他们心里并不思想我记念他们的一切恶; 他们所行的现在缠绕他们,都在我面前。
3 “Suna faranta wa sarki zuciya da muguntarsu, shugabanni kuma da ƙarairayinsu.
他们行恶使君王欢喜, 说谎使首领喜乐。
4 Dukansu mazinata ne suna ƙuna kamar matoya wadda mai gashin burodi ba ya bukata yă tura mata wuta daga cuɗe kullu har kumburinsa.
他们都是行淫的, 像火炉被烤饼的烧热, 从抟面到发面的时候, 暂不使火着旺。
5 A ranar bikin sarkinmu shugabanni sukan bugu da ruwan inabi, yă yi cuɗanya da masu ba’a.
在我们王宴乐的日子, 首领因酒的烈性成病; 王与亵慢人拉手。
6 Zukatansu suna kamar matoya; sukan kusace shi da wayo. Muguwar aniyarsu takan yi ta ci dukan dare; da safe sai ta ƙuna kamar harshen wuta.
首领埋伏的时候,心中热如火炉, 就如烤饼的整夜睡卧, 到了早晨火气炎炎。
7 Dukansu suna da zafi kamar matoya; suna kashe masu mulkinsu. Dukan sarakunansu sukan fāɗi, kuma babu waninsu da yake kira gare ni.
众民也热如火炉, 烧灭他们的官长。 他们的君王都仆倒而死; 他们中间无一人求告我。
8 “Efraim yana cuɗanya da al’ummai; Efraim waina ne mai fāɗi da ba a juye ba.
以法莲与列邦人搀杂; 以法莲是没有翻过的饼。
9 Baƙi sun tsotse ƙarfinsa, amma bai gane ba. Gashi kansa ya cika da furfura, amma bai lura ba.
外邦人吞吃他劳力得来的,他却不知道; 头发斑白,他也不觉得。
10 Girmankan Isra’ila ya ba da shaida a kansa, amma duk da haka bai dawo ga Ubangiji Allahnsa ko yă neme shi ba.
以色列的骄傲当面见证自己, 虽遭遇这一切, 他们仍不归向耶和华—他们的 神, 也不寻求他。
11 “Efraim yana kama da kurciya, marar wayo, marar hankali, yanzu yana kira ga Masar, yanzu yana juyewa ga Assuriya.
以法莲好像鸽子愚蠢无知; 他们求告埃及,投奔亚述。
12 Sa’ad da suka tafi, zan jefa ragata a kansu; zai janye su ƙasa kamar tsuntsayen sararin sama. Sa’ad da na ji suna tafiya tare, zan kama su.
他们去的时候,我必将我的网撒在他们身上; 我要打下他们,如同空中的鸟。 我必按他们会众所听见的惩罚他们。
13 Kaitonsu, domin sun kauce daga gare ni! Hallaka za tă aukar musu, domin sun tayar mini! Na ƙudura in cece su amma suna faɗar ƙarya a kaina.
他们因离弃我,必定有祸; 因违背我,必被毁灭。 我虽要救赎他们,他们却向我说谎。
14 Ba sa yin mini kuka da zuciyarsu amma suna ihu a kan gadajensu. Sukan taru wurin ɗaya don hatsi da ruwan inabi amma su juya mini baya.
他们并不诚心哀求我, 乃在床上呼号; 他们为求五谷新酒聚集, 仍然悖逆我。
15 Na horar da su na kuma ƙarfafa su, amma sun ƙulla mini maƙarƙashiya.
我虽教导他们,坚固他们的膀臂, 他们竟图谋抗拒我。
16 Ba sa juya ga Mafi Ɗaukaka; suna kama da tanƙwararren baka. Za a kashe shugabanninsu da takobi saboda banzan maganganunsu. Saboda wannan za a wulaƙanta su a ƙasar Masar.
他们归向,却不归向至上者; 他们如同翻背的弓。 他们的首领必因舌头的狂傲倒在刀下; 这在埃及地必作人的讥笑。

< Hosiya 7 >