< Farawa 8 >
1 Amma Allah ya tuna da Nuhu da dukan namun jeji da dabbobin da suke tare da shi a cikin jirgi, ya kuma aika da wata iska ta hura dukan duniya, ruwan kuwa ya janye.
神记念挪亚和挪亚方舟里的一切走兽牲畜。 神叫风吹地,水势渐落。
2 Aka toshe maɓuɓɓugan zurfafa da ƙofofin ambaliyar sammai, ruwan sama kuma ya daina saukowa daga sarari.
渊源和天上的窗户都闭塞了,天上的大雨也止住了。
3 Ruwan ya janye a hankali daga ƙasa. A ƙarshen kwanaki ɗari da hamsin ɗin, ruwan ya ragu.
水从地上渐退。过了一百五十天,水就渐消。
4 A rana ta goma sha bakwai ga watan bakwai, jirgin ya sauka a duwatsun Ararat.
七月十七日,方舟停在亚拉腊山上。
5 Ruwan ya ci gaba da janyewa har watan goma. A rana ta fari ga watan goma kuwa ƙwanƙolin duwatsun suka bayyana.
水又渐消,到十月初一日,山顶都现出来了。
6 Bayan kwana arba’in, sai Nuhu ya buɗe tagar jirgin da ya yi,
过了四十天,挪亚开了方舟的窗户,
7 ya saki hankaka. Hankaka ya yi ta kai da kawowa har sai da ruwa ya shanye a duniya.
放出一只乌鸦去;那乌鸦飞来飞去,直到地上的水都干了。
8 Sai ya saki kurciya don yă ga in ruwan ya janye daga doron ƙasa.
他又放出一只鸽子去,要看看水从地上退了没有。
9 Amma kurciyar ba tă sami inda za tă sa ƙafafunta ba gama akwai ruwa a dukan doron ƙasa, saboda haka ta komo wurin Nuhu a jirgi. Ya miƙa hannunsa ya ɗauko kurciyar ya shigar da ita wurinsa a cikin jirgi.
但遍地上都是水,鸽子找不着落脚之地,就回到方舟挪亚那里,挪亚伸手把鸽子接进方舟来。
10 Ya ƙara jira kwana bakwai, sai ya sāke aiken kurciyar daga jirgi.
他又等了七天,再把鸽子从方舟放出去。
11 Sa’ad da kurciya ta komo wurinsa da yamma, sai ga ɗanyen ganyen zaitun da ta tsinko a bakinta! Sa’an nan Nuhu ya san cewa ruwa ya janye daga duniya.
到了晚上,鸽子回到他那里,嘴里叼着一个新拧下来的橄榄叶子,挪亚就知道地上的水退了。
12 Ya ƙara jira kwana bakwai, sai ya sāke aiken kurciyar, amma a wannan ƙaro ba tă komo wurinsa ba.
他又等了七天,放出鸽子去,鸽子就不再回来了。
13 A rana ta fari ga wata na fari wanda Nuhu ya cika shekaru 601, ruwa ya shanye a ƙasa. Sai Nuhu ya buɗe murfin jirgin, ya ga cewa doron ƙasa ya bushe.
到挪亚六百零一岁,正月初一日,地上的水都干了。挪亚撤去方舟的盖观看,便见地面上干了。
14 A ran ashirin da bakwai ga wata na biyu, ƙasa ta bushe ƙaƙaf.
到了二月二十七日,地就都干了。
15 Sa’an nan Allah ya ce wa Nuhu,
神对挪亚说:
16 “Fito daga jirgin, kai da matarka da’ya’yanka maza da matansu.
“你和你的妻子、儿子、儿妇都可以出方舟。
17 Ka fitar da kowane iri halitta mai rai da take tare da kai waje, tsuntsaye, dabbobi, da dukan halittu masu rarrafe a ƙasa, don su yi ta haihuwa, su yi yawa, su ƙaru a duniya.”
在你那里凡有血肉的活物,就是飞鸟、牲畜,和一切爬在地上的昆虫,都要带出来,叫它在地上多多滋生,大大兴旺。”
18 Sai Nuhu ya fito tare da matarsa da’ya’yansa maza da matan’ya’yansa,
于是挪亚和他的妻子、儿子、儿妇都出来了。
19 da kowace irin dabba, da kowane mai rarrafe, da kowane irin tsuntsu, da kowane irin abu da yake tafiya a bisa duniya, suka fito daga jirgi daki-daki bisa ga irinsu.
一切走兽、昆虫、飞鸟,和地上所有的动物,各从其类,也都出了方舟。
20 Sai Nuhu ya gina bagaden hadaya ga Ubangiji, ya ɗiba waɗansu dabbobi da tsuntsaye masu tsabta, ya yi hadaya ta ƙonawa da su a kan bagaden.
挪亚为耶和华筑了一座坛,拿各类洁净的牲畜、飞鸟献在坛上为燔祭。
21 Da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce a zuciyarsa, “Ba zan ƙara la’anta ƙasa saboda mutum ba, ko da yake dukan tunanin zuciyar mutum mugu ne tun yana ƙarami. Ba kuwa zan ƙara hallaka dukan halittu masu rai, kamar yadda na yi ba.
耶和华闻那馨香之气,就心里说:“我不再因人的缘故咒诅地(人从小时心里怀着恶念),也不再按着我才行的灭各种的活物了。
22 “Muddin duniya tana nan, lokacin shuki da na girbi, lokacin sanyi da na zafi, lokacin damina da na rani, dare da rana ba za su daina ba.”
地还存留的时候,稼穑、寒暑、冬夏、昼夜就永不停息了。”

A Dove is Sent Forth from the Ark