< Farawa 43 >
1 A yanzu, yunwa ta yi tsanani a ƙasar.
那地的饥荒甚大。
2 Saboda haka sa’ad da suka cinye dukan hatsin da suka kawo daga Masar, mahaifinsu ya ce musu, “Ku koma, ku sayo mana ƙarin abinci.”
他们从埃及带来的粮食吃尽了,他们的父亲就对他们说:“你们再去给我籴些粮来。”
3 Amma Yahuda ya ce masa, “Mutumin ya gargaɗe mu sosai cewa, ‘Ba za ku sāke ganin fuskata ba sai in ɗan’uwanku yana tare da ku.’
犹大对他说:“那人谆谆地告诫我们说:‘你们的兄弟若不与你们同来,你们就不得见我的面。’
4 In za ka aika da ɗan’uwanmu tare da mu, za mu gangara mu sayo maka abinci.
你若打发我们的兄弟与我们同去,我们就下去给你籴粮;
5 Amma in ba za ka aika da shi ba, ba za mu gangara ba, gama mutumin ya ce mana, ‘Ba za ku sāke ganin fuskata ba sai ko in ɗan’uwanku yana tare da ku.’”
你若不打发他去,我们就不下去,因为那人对我们说:‘你们的兄弟若不与你们同来,你们就不得见我的面。’”
6 Isra’ila ya yi tambaya, “Me ya sa kuka kawo wannan damuwa a kaina ta wurin faɗa wa mutumin cewa kuna da wani ɗan’uwa?”
以色列说:“你们为什么这样害我,告诉那人你们还有兄弟呢?”
7 Suka amsa, “Mutumin ya yi mana tambaya sosai game da kanmu da iyalinmu. Ya tambaye mu, ‘Mahaifinku yana da rai har yanzu? Kuna da wani ɗan’uwa?’ Mu dai mun amsa tambayoyinsa ne. Ta yaya za mu sani zai ce, ‘Ku kawo ɗan’uwanku a nan’?”
他们回答说:“那人详细问到我们和我们的亲属,说:‘你们的父亲还在吗?你们还有兄弟吗?’我们就按着他所问的告诉他,焉能知道他要说‘必须把你们的兄弟带下来’呢?”
8 Sa’an nan Yahuda ya ce wa Isra’ila mahaifinsa, “Ka aika saurayin tare da ni za mu kuwa tafi nan da nan, saboda mu da’ya’yanmu mu rayu, kada mu mutu.
犹大又对他父亲以色列说:“你打发童子与我同去,我们就起身下去,好叫我们和你,并我们的妇人孩子,都得存活,不至于死。
9 Ni kaina zan tabbatar da lafiyarsa; na ɗauki lamuninsa, a hannuna za ka neme shi. In ban dawo da shi gare ka, in sa shi nan a gabanka ba, zan ɗauki laifin a gabanka dukan kwanakina.
我为他作保;你可以从我手中追讨,我若不带他回来交在你面前,我情愿永远担罪。
10 Ai, da ba mun jinkirta ba, da mun komo har sau biyu.”
我们若没有耽搁,如今第二次都回来了。”
11 Sa’an nan mahaifinsu Isra’ila ya ce musu, “In dole ne a yi haka, to, sai ku yi. Ku sa waɗansu amfani mafi kyau na ƙasar a buhunanku, ku ɗauka zuwa wurin mutumin a matsayin kyauta, da ɗan man ƙanshi na shafawa, da kuma’yar zuma, da kayan yaji, da ƙaro, da tsabar citta da kuma almon.
他们的父亲以色列说:“若必须如此,你们就当这样行:可以将这地土产中最好的乳香、蜂蜜、香料、没药、榧子、杏仁都取一点,收在器具里,带下去送给那人作礼物,
12 Ku ɗauki ninki biyu na yawan azurfa tare da ku, gama dole ku mayar da azurfan da aka sa a cikin bakunan buhunanku. Mai yiwuwa an yi haka a kuskure ne.
又要手里加倍地带银子,并将归还在你们口袋内的银子仍带在手里;那或者是错了。
13 Ku ɗauki ɗan’uwanku kuma ku koma wurin mutumin nan da nan.
也带着你们的兄弟,起身去见那人。
14 Bari Allah Maɗaukaki yă nuna muku alheri a gaban mutumin saboda yă bar ɗan’uwanku da Benyamin su dawo tare da ku. Ni kuwa, in na yi rashi, na yi rashi.”
但愿全能的 神使你们在那人面前蒙怜悯,释放你们的那弟兄和便雅悯回来。我若丧了儿子,就丧了吧!”
15 Saboda haka mutanen suka ɗauki kyautar, da kuma kuɗin da ya ninka na farko. Suka kuma ɗauki Benyamin, suka gaggauta suka gangara zuwa Masar suka kuma gabatar da kansu ga Yusuf.
于是,他们拿着那礼物,又手里加倍地带银子,并且带着便雅悯,起身下到埃及,站在约瑟面前。
16 Sa’ad da Yusuf ya ga Benyamin tare da su, sai ya ce wa mai hidimar gidansa, “Ka shigar da mutanen cikin gida, ka yanka dabba ka shirya, gama mutanen za su ci abincin rana tare da ni.”
约瑟见便雅悯和他们同来,就对家宰说:“将这些人领到屋里。要宰杀牲畜,预备筵席,因为晌午这些人同我吃饭。”
17 Mutumin ya yi kamar yadda Yusuf ya faɗa masa, ya kuwa ɗauki mutanen zuwa gidan Yusuf.
家宰就遵着约瑟的命去行,领他们进约瑟的屋里。
18 Mutanen dai suka firgita sa’ad da aka ɗauke su zuwa gidansa. Suka yi tunani, “An kawo mu nan ne saboda azurfan da aka sa a cikin buhunanmu da farko. Yana so yă fāɗa mana, yă kuma sha ƙarfinmu, yă ƙwace mu kamar bayi, yă kuma kwashe jakunanmu.”
他们因为被领到约瑟的屋里,就害怕,说:“领我们到这里来,必是因为头次归还在我们口袋里的银子,找我们的错缝,下手害我们,强取我们为奴仆,抢夺我们的驴。”
19 Saboda haka suka je wurin mai yin wa Yusuf hidima, suka yi masa magana a bakin ƙofar gida.
他们就挨近约瑟的家宰,在屋门口和他说话,
20 Suka ce, “Ranka yă daɗe, mun zo nan ƙaro na farko don mu saya abinci,
说:“我主啊,我们头次下来实在是要籴粮。
21 amma a inda muka tsaya don mu kwana, da muka buɗe buhunanmu sai kowannenmu ya sami azurfansa daidai a bakin buhunsa. Saboda haka ga kuɗin a hannunmu, mun sāke komowa da su.
后来到了住宿的地方,我们打开口袋,不料,各人的银子,分量足数,仍在各人的口袋内,现在我们手里又带回来了。
22 Mun kuma kawo ƙarin azurfa tare da mu don mu saya abinci. Ba mu san wa ya sa azurfanmu a cikin buhunanmu ba.”
另外又带下银子来籴粮。不知道先前谁把银子放在我们的口袋里。”
23 Sai mai hidimar ya ce, “Ba kome, kada ku ji tsoro. Allahnku, Allahn mahaifinku ne ya ba ku dukiyar a cikin buhunanku; ni dai, na karɓi azurfanku.” Sa’an nan ya fitar musu da Simeyon.
家宰说:“你们可以放心,不要害怕,是你们的 神和你们父亲的 神赐给你们财宝在你们的口袋里;你们的银子,我早已收了。”他就把西缅带出来,交给他们。
24 Mai yin hidimar ya ɗauki mutane zuwa gidan Yusuf ya ba su ruwa su wanke ƙafafunsu, ya kuma tanada wa jakunansu abinci.
家宰就领他们进约瑟的屋里,给他们水洗脚,又给他们草料喂驴。
25 Suka shirya kyautansu domin isowar Yusuf da rana, gama sun ji cewa zai ci abinci a nan.
他们就预备那礼物,等候约瑟晌午来,因为他们听见要在那里吃饭。
26 Sa’ad da Yusuf ya zo gida, sai suka ba shi kyautai da suka kawo, suka rusuna a gabansa har ƙasa.
约瑟来到家里,他们就把手中的礼物拿进屋去给他,又俯伏在地,向他下拜。
27 Ya tambaye su, yaya suke, sa’an nan ya ce, “Yaya tsohon nan mahaifinku da kuka faɗa mini? Yana da rai har yanzu?”
约瑟问他们好,又问:“你们的父亲—就是你们所说的那老人家平安吗?他还在吗?”
28 Suka amsa, “Bawanka mahaifinmu yana da rai har yanzu da kuma ƙoshin lafiya.” Suka kuma rusuna suka yi mubaya’a.
他们回答说:“你仆人—我们的父亲平安;他还在。”于是他们低头下拜。
29 Da ya ɗaga idanu, sai ya ga ɗan’uwansa Benyamin, ɗan mahaifiyarsa, sai ya yi tambaya, “Wannan ne ƙaramin ɗan’uwanku, wanda kuka faɗa mini a kai?” Ya kuma ce, “Allah yă yi maka albarka, ɗana.”
约瑟举目看见他同母的兄弟便雅悯,就说:“你们向我所说那顶小的兄弟就是这位吗?”又说:“小儿啊,愿 神赐恩给你!”
30 Saboda motsi mai zurfi da zuciyarsa ta yi da ganin ɗan’uwansa, sai Yusuf ya gaggauta ya fita, ya nemi wuri yă yi kuka. Ya shiga ɗakinsa ya yi kuka a can.
约瑟爱弟之情发动,就急忙寻找可哭之地,进入自己的屋里,哭了一场。
31 Bayan ya wanke fuskarsa, sai ya fito ya daure, ya umarta, “A kawo abinci.”
他洗了脸出来,勉强隐忍,吩咐人摆饭。
32 Sai aka raba musu abinci, nasa shi kaɗai su kuma su kaɗai, domin Masarawa ba sa cin abinci tare da Ibraniyawa, gama wannan abin ƙyama ne ga Masarawa.
他们就为约瑟单摆了一席,为那些人又摆了一席,也为和约瑟同吃饭的埃及人另摆了一席,因为埃及人不可和希伯来人一同吃饭;那原是埃及人所厌恶的。
33 Aka zaunar da’yan’uwan Yusuf a gabansa bisa ga shekarunsu, daga ɗan fari zuwa auta.’Yan’uwan kuwa suka duddubi juna suna mamaki.
约瑟使众弟兄在他面前排列坐席,都按着长幼的次序,众弟兄就彼此诧异。
34 Daga teburin da yake a gaban Yusuf aka riƙa ɗibar rabonsu ana kai musu, amma rabon Benyamin ya yi biyar ɗin na kowannensu. Suka kuwa sha, suka yi murna tare da shi.
约瑟把他面前的食物分出来,送给他们;但便雅悯所得的比别人多五倍。他们就饮酒,和约瑟一同宴乐。