< Ezra 7 >

1 Bayan waɗannan abubuwa, a zamanin Artazerzes sarkin Farisa, sai Ezra ɗan Serahiya, ɗan Azariya, ɗan Hilkiya,
Après ces événements, sous le règne d’Artaxerxès, roi de Perse, Esdras, fils de Saraïas, fils d’Azarias, fils d’Helcias,
2 ɗan Shallum, ɗan Zadok, ɗan Ahitub,
fils de Sellum, fils de Sadoc, fils d’Achitob,
3 ɗan Amariya, ɗan Azariya, ɗan Merahiyot,
fils d’Amarias, fils d’Azarias, fils de Maraïoth,
4 ɗan Zerahiya, ɗan Uzzi, ɗan Bukki,
fils de Zarahias, fils d’Ozi, fils de Bocci,
5 ɗan Abishuwa, ɗan Finehas, ɗan Eleyazar, ɗan Haruna babban firist.
fils d’Abisué, fils de Phinées, fils d’Eléazar, fils d’Aaron, le grand prêtre, —
6 Shi Ezra ɗin ya zo daga Babilon. Shi malami ne ya kuma san Dokar Musa sosai wadda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya bayar. Sarki ya ba shi duk abin da ya roƙa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi.
cet Esdras monta de Babylone: c’était un scribe versé dans la loi de Moïse, qu’a donnée Yahweh, le Dieu d’Israël. Comme la main de Yahweh, son Dieu, était sur lui, le roi lui accorda tout ce qu’il avait demandé.
7 Waɗansu Isra’ilawa, haɗe da firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da masu aiki a haikali su ma suka zo Urushalima a shekara ta bakwai a zamanin mulkin sarki Artazerzes.
Plusieurs des enfants d’Israël, des prêtres et des lévites, des chantres, des portiers et des Nathinéens montèrent aussi à Jérusalem, la septième année du roi Artaxerxès.
8 Ezra ya iso Urushalima a wata na biyar na shekara ta bakwai na kama mulkin sarkin.
Esdras arriva à Jérusalem le cinquième mois de la septième année du roi.
9 Ya fara tafiyarsa daga Babilon a rana ta farko ga watan farko, ya kuma iso Urushalima a rana ta farko ga watan biyar, gama alherin Allahnsa yana tare da shi.
C’est le premier jour du premier mois qu’il commença à monter de Babylone, et c’est le premier jour du cinquième mois qu’il arriva à Jérusalem, la main bienfaisante de son Dieu étant sur lui.
10 Gama Ezra ya miƙa kansa ga bincike da kuma kiyaye Dokar Ubangiji, da kuma koya wa Isra’ilawa dokoki da kuma umarnan Ubangiji.
Car Esdras avait appliqué son cœur à étudier la loi de Yahweh, à la mettre en pratique, et à enseigner en Israël les préceptes et les ordonnances.
11 Ga wasiƙar da sarki Artazerzes ya ba Ezra wanda yake firist da kuma malami, mutumin da yake cike da sani game da dokoki da kuma umarnan Ubangiji wa Isra’ila.
Voici la copie de la lettre que le roi Artaxerxès donna à Esdras, le prêtre et le scribe, scribe instruit des paroles de la loi de Yahweh et de ses préceptes, concernant Israël:
12 Artazerzes, sarkin sarakuna. Zuwa ga Ezra firist, malamin Dokar Allah na sama. Gaisuwa.
« Artaxerxès, roi des rois, à Esdras, prêtre et scribe versé dans la loi du Dieu du ciel, etc.
13 Yanzu ina ba da umarni cewa duk wani mutumin Isra’ilan da yake cikin mulkina, haɗe da firistoci, da Lawiyawa, da suke so su tafi tare da kai zuwa Urushalima za su iya tafiya.
J’ai donné ordre pour que tous ceux du peuple d’Israël, de ses prêtres et de ses lévites, résidant dans mon royaume, qui désirent aller à Jérusalem, y aillent avec toi.
14 Sarki ne da mashawartansa guda bakwai suka aike ka don ka je ka ga halin da Yahuda da Urushalima suke ciki game da dokokin Allahnka, waɗanda suke a hannunka.
Car tu es envoyé par le roi et ses sept conseillers pour inspecter Juda et Jérusalem d’après la loi de ton Dieu, laquelle est dans ta main,
15 Za ka kuma tafi da zinariya da azurfa waɗanda sarki da mashawartansa suka ba da kyautar yardar rai ga Allah na Isra’ila, wanda haikalinsa ke a Urushalima,
et pour porter l’argent et l’or que le roi et ses conseillers ont spontanément offerts au Dieu d’Israël, dont la demeure est à Jérusalem,
16 haɗe da duk zinariya da azurfan da za ka iya samu a Babilon, da kuma duk bayarwar yardar rai daga mutane da firistoci, domin haikalin Allahnsu da yake a Urushalima.
ainsi que tout l’or et l’argent que tu trouveras dans toute la province de Babylone, avec les dons volontaires du peuple et des prêtres, librement offerts pour la maison de leur Dieu à Jérusalem.
17 Ka tabbata ka yi amfani da kuɗin nan don ka sayi bijimai, da raguna, da’yan raguna, da hadayu na gari, da na sha, ka kuma miƙa su a kan bagade na haikalin Allahnka a Urushalima.
C’est pourquoi tu auras soin d’acheter avec cet argent des taureaux, des béliers, des agneaux, et ce qui est nécessaire pour les oblations et les libations qui les accompagnent, et tu les offriras sur l’autel de la maison de votre Dieu, qui est à Jérusalem.
18 Sa’an nan kai da’yan’uwanka Yahudawa ku yi abin da kuka ga ya fi kyau da sauran zinariya da azurfa ɗin bisa ga nufin Allah.
Vous ferez, avec le reste de l’argent et de l’or, ce qui vous paraîtra bon, à toi et à tes frères, en vous conformant à la volonté de votre Dieu.
19 Ka kai wa Allah na Urushalima duk kayan da aka ba ka amanarsu don yin sujada a haikalin Allahnka.
Dépose devant le Dieu de Jérusalem les ustensiles qui te sont donnés pour le service de la maison de ton Dieu.
20 Duk kuma wani abin da ake bukata domin haikalin Allahnka, daga ɗakunan ajiya sarki za ka fitar da kuɗin.
Et le reste de ce qui est nécessaire à la maison de ton Dieu, et que tu auras à fournir, tu le fourniras après l’avoir reçu de la maison des trésors du roi.
21 Yanzu fa ni, Sarki Artazerzes, ina ba da umarni ga kowane ma’aji na Kewayen Kogin Yuferites su tanada duk abin da Ezra firist, wanda kuma yake malamin Dokar Allah na sama zai bukaci,
Et moi, le roi Artaxerxès, je donne ordre à tous les trésoriers d’au delà du fleuve que tout ce qu’Esdras, prêtre et scribe, versé dans la loi du Dieu du ciel, vous demandera, soit exactement exécuté:
22 har zuwa talenti ɗari na azurfa, da mudu ɗari na alkama, da garwa ɗari na ruwan inabi, da garwa ɗari na man zaitun, da kuma gishiri ba iyaka.
jusqu’à cent talents d’argent, cent cors de froment, cent baths de vin, cent baths d’huile, et du sel à discrétion.
23 A yi duk abin da Allah na sama ya ce don haikalin Allah na sama, sai a yi shi da himma. Me zai sa a jawo wa sarki da’ya’yansa fushin Allah?
Que tout ce qui est ordonné par le Dieu du ciel soit ponctuellement accompli pour la maison du Dieu du ciel, afin que sa colère ne vienne pas sur le royaume du roi et de ses fils.
24 Ku kuma san cewa, ba ku da ikon sa firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofin haikali, da masu aiki a gidan Allah, ko waɗansu masu aiki a haikali su biya haraji, ko kuɗin shiga.
Nous vous faisons savoir aussi qu’en ce qui concerne tous les prêtres, lévites, chantres, portiers, Nathinéens et serviteurs quelconques de cette maison de Dieu, il n’est pas permis de lever sur eux ni impôt, ni tribut, ni droit de passage.
25 Kai kuma Ezra, bisa ga hikimar da Allah ya ba ka, sai ka zaɓi mahukunta da alƙalai waɗanda za su zama masu yanke hukunci ga dukan mutanen Kewayen Kogin Yuferites, duk waɗanda suka san dokokin Allahnka, ka kuma koya wa duk waɗanda ba su san dokokin ba.
Et toi, Esdras, selon la sagesse de ton Dieu, qui est dans ta main, établis des juges et des magistrats qui rendent la justice à tout le peuple d’au delà du fleuve, à tous ceux qui connaissent les lois de ton Dieu, et enseigne-les à ceux qui ne les connaissent pas.
26 Ba shakka duk wanda bai yi biyayya da dokokin Allahnka ba, da kuma dokokin sarki ba dole a yanke masa hukuncin kisa, ko hukuncin kora, ko hukuncin raba shi da mallakarsa, ko kuma hukuncin kulle shi a kurkuku.
Quiconque n’exécutera pas la loi de ton Dieu et la loi du roi, qu’il soit fait de lui exacte justice, soit par la mort, soit par le bannissement, soit par une amende, soit par la prison. »
27 Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na kakanninmu, ya taɓa zuciyar sarki don yă kawo ɗaukaka ga haikalin Allah a Urushalima ta wannan hanya.
Béni soit Yahweh, le Dieu de nos pères, qui a mis ainsi au cœur du roi de glorifier la maison de Yahweh qui est à Jérusalem,
28 Wanda kuma ya sa na sami tagomashi a gaban sarki da mashawartansa, da kuma duk manyan masu muƙami nasa. Gama Ubangiji Allahna yana tare da ni, sai na sami ƙarfin hali na tattara shugabannin mutane daga Isra’ila, don mu tafi tare.
et qui a tourné sur moi la bienveillance du roi, de ses conseillers et de tous les plus puissants officiers du roi! Et je pris courage parce que la main de Yahweh mon Dieu était sur moi, et je rassemblai les chefs d’Israël, afin qu’ils partissent avec moi.

< Ezra 7 >