< Ezekiyel 48 >
1 “Ga kabilan, a jere bisa ga sunayensu. “A iyaka ta arewa, Dan zai sami rabo; zai bi hanyar Hetlon zuwa Lebo Hamat. Hazar-Enan da iyakar arewancin Damaskus kusa da Hamat za tă zama sashen iyakarsa a wajen gabas zuwa wajen yamma.
“Here is a list of the tribes of Israel [and the territory that each tribe is to receive]: [The tribe of] Dan will be allotted land at the northern boundary [of Israel]: It will extend east from the Mediterranean Sea east to Hethlon [city], then from there to Hamath Pass, and on to [the town of] Hazar-Enan south of Damascus, between Damascus and Hamath. The tribe of Dan will receive land on the northern border [of Israel] from the eastern end [of the country] west to the [Mediterranean] Sea.
2 Asher zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Dan daga gabas zuwa yamma.
South of their land will be the territory [for the tribe] of Asher.
3 Naftali zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Asher daga gabas zuwa yamma.
South of their land will be the territory [for the tribe] of Naphtali.
4 Manasse zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Naftali daga gabas zuwa yamma.
South of their land will be the territory [for the tribe] of Manasseh.
5 Efraim zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Manasse daga gabas zuwa yamma.
South of their land will be the territory [for the tribe] of Ephraim.
6 Ruben zai sami rabo; zai yi iyaka da Efraim daga gabas zuwa yamma.
South of their land will be the territory [for the tribe] of Reuben.
7 Yahuda zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Ruben daga gabas zuwa yamma.
South of their land will be the territory [for the tribe] of Judah.
8 “Kusa da yankin Yahuda daga gabas zuwa yamma zai zama rabon da za ku bayar a matsayin kyauta ta musamman. Faɗinsa zai zama kamu 25,000, tsawonsa kuma zai zama daidai da tsawon yankunan kabilu daga gabas zuwa yamma; wuri mai tsarki zai kasance a tsakiyar wannan yanki.
South of their land will be an area set apart for special use. The temple will be in the center of that area.
9 “Tsawon rabo na musamman da za ku bayar ga Ubangiji zai zama kamu 25,000, fāɗinsa kuma kamu 10,000.
It must be (8.3 miles/13.3 km.) long and (6.7 miles/10.6 km.) wide.
10 Wannan ne zai zama tsattsarkan rabo domin firistoci. Tsawon zai zama kamu 25,000 a wajen arewa, fāɗin kuma kamu 10,000 wajen yamma, kamu 10,000 zai zama fāɗinsa a wajen gabas, tsawonsa a wajen kudu zai zama kamu 25,000. A tsakiyarsa ne wuri mai tsarki na Ubangiji zai kasance.
For the priests, there must be a strip of land (8.3 miles/13.3 km.) long and (3.3 miles/5.3 km.) wide. The temple will be in the center of that area.
11 Wannan zai zama na keɓaɓɓun firistoci, zuriyar Zadok, waɗanda suka yi aminci cikin hidimata ba su kuwa karkata kamar yadda Lawiyawa suka yi sa’ad da Isra’ilawa suka karkace ba.
That area is for the priests who are descendants of Zadok. They are ones who served me faithfully and did not turn away from me, like most of the descendants of Levi and the other Israeli people did.
12 Zai zama kyauta ta musamman a gare su daga tsattsarkan rabon ƙasar, kusa da yankin Lawiyawa.
When the land is distributed, that area must be given to the priests; it is land that is very sacred. It will be next to the land that will be given to the other descendants of Levi.
13 “Dab da yankin firistoci, Lawiyawa za su sami rabo mai tsawon kamu 25,000, fāɗin kuma kamu 10,000. Tsawonsa gaba ɗaya zai zama kamu 25,000, fāɗinsa kuma kamu 10,000.
The land that will be allotted to the [other] descendants of Levi will be the same size as the land allotted to the priests. So together, those two portions of land will be (8.3 miles/13.3 km.) long and (6.6 miles/10.6 km.) wide.
14 Ba za su sayar da shi ko su musayar da wani sashensa ba. Wannan shi ne mafi kyau na ƙasar ba kuma za a jinginar da ita ga wani ba, gama mai tsarki ce ga Ubangiji.
None of this special land will ever be permitted to be sold or traded or used by other people, because it belongs to me, Yahweh. It is set apart for me.
15 “Sauran wurin da ya rage mai fāɗin kamu 5,000 da tsawon kamu 25,000 zai zama don amfanin kowa a birnin, don gidaje da wurin kiwo. Birnin zai kasance a tsakiyar wurin da ya ragen nan
The rest [of that sacred area, a strip of land] (8.3 miles/13.3 km.) long and (1.7 miles/2.65 km.) wide will be allotted for other people to use. It will be land where they will be permitted to build homes and have pasturelands. There will be a city at the center.
16 zai kuwa kasance da wannan awon, a wajen arewa kamu 45,000, wajen kudu kamu 45,000, wajen gabas kamu 45,000, wajen kudu kuma kamu 45,000.
The city will be square, (1.5 miles/2.4 km.) on each side.
17 Wurin kiwo don birnin zai zama kamu 250 a wajen arewa, kamu 250 a wajen kudu, kamu 250 a wajen gabas da kuma kamu 250 a wajen yamma.
Around the city there will be an area for farming, that will be (150 yards/135 meters) in each direction.
18 Tsawon abin da ya rage a wurin, dab da tsattsarkan rabo, zai zama kamu 10,000 wajen gabas, kamu 10,000 kuma wajen yamma. Amfanin da zai bayar zai tanada abinci don ma’aikatan birnin.
Outside the city, to the east and to the west, there will be a farming area. It will extend (3 miles/4.8 km.) to the east and (3 miles/4.8 km.) to the west. [Men who work there] will produce food for the people who work in the city.
19 Masu aiki daga birnin waɗanda suka nome ta za su fito daga dukan kabilan Isra’ila.
[Some of] those who come from the various Israeli tribes to work in the city may also work on the farmland.
20 Dukan rabon zai zama murabba’i, kamu 25,000 kowane gefe. A matsayin kyauta ta musamman za ku keɓe tsattsarkan rabo, haka ma za ku yi da mallakar birnin.
That entire special area, including the sacred lands and the city, will be a square that is (8.3 miles/13.3 km.) on each side.
21 “Abin da ya rage a kowane gefe na wurin zai zama tsattsarkan rabo kuma mallakar birnin za tă zama ta sarki. Zai miƙe wajen gabas daga kamu 25,000 na tsattsarkan rabo zuwa iyakar da take wajen gabashin iyaka, da kuma a wajen yamma kamu 25,000 zuwa iyakar da take a wajen yamma. Dukan wuraren nan da suke hannun riga da rabon kabilan zai zama na sarki, tsattsarkan rabon tare da wuri mai tsarkin za su kasance a tsakiyarsu.
The areas to the east and to the west of the sacred area and the city will belong to the king. One area will extend east to the eastern boundary of Israel and the other will extend west to the Mediterranean Sea. The sacred area in which the temple is located will be in the middle.
22 Ta haka mallakar Lawiyawa da mallakar birnin za su kasance a tsakiyar wurin da yake na sarki. Wurin da yake na sarki zai kasance tsakanin iyakar Yahuda da iyakar Benyamin.
The area that belongs to the king will be between the land [of the tribe] of [to the north] and the land [of the tribe] of Benjamin [to the south].
23 “Game da sauran kabilun kuwa, “Benyamin zai sami rabo; zai miƙe daga wajen gabas zuwa wajen yamma.
South of that special area, each of the other tribes must be allotted one portion of land that extends from the eastern [boundary of Israel] west [to the Mediterranean Sea]. [Beginning at the north] will be land for [the tribe of] Benjamin.
24 Simeyon zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Benyamin daga gabas zuwa yamma.
South of their land will be the territory for [the tribe of] Simeon.
25 Issakar zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Simeyon daga gabas zuwa yamma.
South of their land will be the territory for [the tribe of] Issachar.
26 Zebulun zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Issakar daga gabas zuwa yamma.
South of their land will be the territory for [the tribe of] Zebulun.
27 Gad zai sami rabo; zai yi iyaka da yankin Zebulun daga gabas zuwa yamma.
South of their land will be the territory for [the tribe of] Gad.
28 Iyakar kudu ta Gad za tă miƙe kudu daga Tamar zuwa ruwan Meriba Kadesh, sa’an nan ta bi Rafin Masar zuwa Bahar Rum.
The southern boundary of [the tribe of] Gad will extend south from Tamar to the springs at Meribah-Kadesh, and from there [to the west] along the dry riverbed at the border of Egypt to the Mediterranean Sea.
29 “Wannan ce ƙasar da za ku raba gādo ga kabilan Isra’ila, kuma wannan ne zai zama rabonsu,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
That is the land that you must allot to the tribes of Israel, to belong to them permanently. [That is what I], Yahweh the Lord, declare.”
30 “Waɗannan za su zama ƙofofin birnin. “Farawa da gefen arewa, wanda yake da tsawon kamu 4,500
These will be the exits from the city: On the north side, which will be (1.5 miles/2.4 km.) long,
31 za a ba wa ƙofofin birnin sunaye kabilan Isra’ila. Ƙofofi uku a gefen arewa za su zama ƙofar Ruben, ƙofar Yahuda da ƙofar Lawi.
there must be three gates; each one will have the name of one of the tribes of Israel. The first one will be named for Reuben, the next for Judah, the next for Levi.
32 A gefen gabas, wanda yake da tsawon kamu 4,500 zai kasance da ƙofofi uku, ƙofar Yusuf, ƙofar Benyamin da ƙofar Dan.
On the east side, [also] (1.5 miles/2.4 km.) long, will be gates named for Joseph, Benjamin, and Dan.
33 A gefen kudu, wanda yake da tsawon kamu 4,500, zai kasance da ƙofofi uku, ƙofar Simeyon, ƙofar Issakar da ƙofar Zebulun.
On the south side, [also] (1.5 miles/2.4 km.) long, will be gates named for Simeon, Issachar, and Zebulun.
34 A gefen yamma, wanda yake da tsawon kamun 4,500, zai kasance da ƙofofi uku, ƙofar Gad, ƙofar Asher da kuma ƙofar Naftali.
On the west side, [also] (1.5 miles/2.4 km.) long, will be gates named for Gad, Asher, and Naphtali.
35 “Duk nisan wurare kewaye da birnin zai zama kamu 18,000 ne. “Sunan birnin kuwa daga wannan lokaci zai zama, ‘Ubangiji yana a nan.’”
[So] the distance around the city will thus be (6 miles/9.6 km.). And from that time on, the name of the city will be ‘Yahweh Is There’.’