< Ezekiyel 31 >

1 A shekara ta goma sha ɗaya, a wata na uku a rana ta farko, maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
And it comes to pass, in the eleventh year, in the third [month], on the first of the month, a word of YHWH has been to me, saying,
2 “Ɗan mutum, faɗa wa Fir’auna sarkin Masar da jama’arsa cewa, “‘Da wa za a kwatanta girmanka?
“Son of man, say to Pharaoh king of Egypt, and to his multitude: To whom have you been like in your greatness?
3 Ka dubi Assuriya, ta taɓa zama kamar al’ul a Lebanon da rassa masu kyau suna inuwartar da kurmi; ya yi tsayi ainun kansa ya kai cikin gizagizai.
Behold, Asshur, a cedar in Lebanon, Beautiful in branch, and shading bough, and high in stature, And its foliage has been between thickets.
4 Ruwa ya sa ya yi girma, zurfafan maɓulɓulai sun sa ya yi tsayi; rafuffuka suna gudu kewaye da tushensa yana aika da rafuffukansa zuwa dukan itatuwan kurmi.
Waters have made it great, The deep has exalted him with its flowings, Going around its planting, And it has sent forth its conduits to all trees of the field.
5 Saboda haka ya yi tsayi fiye da sauran itatuwan kurmi; rassansa suka ƙaru suka yi tsayi, suka bazu saboda yalwar ruwaye.
Therefore his stature has been higher than all trees of the field, And his boughs are multiplied, and his branches are long, Because of many waters in his shooting forth.
6 Dukan tsuntsayen sararin sama suka yi sheƙa a rassansa, dukan namun jeji suka haihu a ƙarƙashin rassansa; dukan al’ummai suka zauna a inuwarsa.
Every bird of the heavens has made a nest in his boughs, And every beast of the field has brought forth under his branches, And all great nations dwell in his shade.
7 Yana da girma a kyau, da dogayen rassansa da ya baza, gama saiwoyinsa sun nutse can ƙasa har cikin yalwar ruwaye.
And he is beautiful in his greatness, In the length of his thin shoots, For his root has been by great waters.
8 Al’ul a cikin lambun Allah ba su kai shi ba, balle itatuwan kasharina su kai rassansa, ko itatuwan durumi su kai rassansa, ko itace a lambun Allah ya kai kyansa.
Cedars have not hid him in the garden of God, Firs have not been like to his boughs, And plane-trees have not been as his branches, No tree in the garden of God has been like to him in his beauty,
9 Na sa ya yi kyau da yalwar rassa, abin ƙyashi na dukan itatuwan Eden a lambun Allah.
I have made him beautiful in the multitude of his thin shoots, And all trees of Eden that [are] in the garden of God envy him.
10 “‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin ya yi tsayi, kansa kuma ya kai cikin gizagizai, kuma domin ya yi fariya saboda tsayinsa,
Therefore, thus said Lord YHWH: Because that you have been high in stature, And he yields his foliage between thickets, And his heart is high in his haughtiness,
11 na miƙa shi ga mai mulkin al’ummai, don yă sāka masa gwargwadon muguntarsa. Na jefar da shi a gefe,
I give him into the hand of a god of nations, He deals severely with him, In his wickedness I have cast him out.
12 kuma baƙi mafi mugunta na al’ummai suka sare shi suka bar shi. Rassansa sun fāɗi a kan duwatsun da suke cikin dukan kwaruruka; rassansa kuma sun kakkarye, sun fāɗi a cikin dukan magudanan ruwa na ƙasa. Dukan al’umman duniya suka fito daga ƙarƙashin inuwarsa suka bar shi.
And strangers cut him off, The terrible of nations, and they leave him, His thin shoots have fallen on the mountains and in all valleys, And his boughs are broken at all streams of the land, And all peoples of the land go down from his shade, and they leave him.
13 Dukan tsuntsaye sararin sama suka zauna a itacen da ya fāɗi, dukan namun jeji kuma suna cikin rassansa.
Every bird of the heavens dwells on his ruin, And all beasts of the field have been on his boughs,
14 Saboda haka ba wani daga cikin itatuwan da suke kusa da ruwan da zai taɓa yin fariyar tsawonsa, har kawunansu su kai cikin gizagizai. Ba wani daga cikin itatuwan da ya sha ruwa sosai da zai taɓa yi wannan tsayi; duk an bashe su ga mutuwa, zuwa can ƙasa, a cikin matattu, tare da waɗanda suka gangara zuwa rami.
In order that none of the trees of the waters May become haughty because of their stature, Nor give their foliage between thickets, Nor any drinking waters stand up to them in their haughtiness, For all of them are given up to death, To the lower earth, In the midst of the sons of men, To those going down to the pit.
15 “‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar da aka yi ƙasa da shi zuwa kabari na rufe zurfafa maɓulɓulai da makoki dominsa; na janye rafuffukansa, aka kuma hana yalwan ruwansa. Saboda shi na rufe Lebanon da baƙin ciki, dukan itatuwan kurmi suka bushe. (Sheol h7585)
Thus said Lord YHWH: I have caused mourning in the day of his going down to Sheol, I have covered the deep over him, and diminish its flowings, And many waters are restrained, And I make Lebanon black for him, And all trees of the field [have been] a covering for him. (Sheol h7585)
16 Na sa al’ummai suka yi rawar jiki da jin ƙarar fāɗuwarsa sa’ad da na yi ƙasa da shi zuwa kabari tare da waɗanda suka gangara rami. Sai dukan itatuwan Eden, zaɓaɓɓu da kuma mafi kyau na Lebanon, dukan itatuwan da aka yi musu banruwa, sun ta’azantu a ƙarƙashin ƙasa. (Sheol h7585)
I have caused nations to shake at the sound of his fall, In My causing him to go down to Sheol, With those going down to the pit, And all trees of Eden are comforted in the lower earth, The choice and good of Lebanon—All drinking waters. (Sheol h7585)
17 Waɗanda suka zauna a inuwarsa, dukan masu tarayyarsa a cikin al’ummai, su ma sun gangara zuwa kabari tare da shi, sun haɗu da waɗanda aka kashe da takobi. (Sheol h7585)
Those with him have also gone down to Sheol, To the pierced of the sword, And—his arm—they dwelt in his shade in the midst of nations. (Sheol h7585)
18 “‘Da wa cikin itatuwan Eden za a kwatanta da kai cikin girma da daraja? Duk da haka kai ma, za a yi ƙasa da kai tare da itatuwan Eden zuwa ƙarƙashin ƙasa; za ka kwanta a cikin marasa kaciya, tare da waɗanda aka kashe da takobi. “‘Fir’auna ke nan da dukan jama’arsa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’”
To whom have you been thus like, In glory and in greatness among the trees of Eden? And you have been brought down with the trees of Eden, To the lower earth, You lie in the midst of the uncircumcised, With the pierced of the sword. This [is] Pharaoh, and all his multitude, A declaration of Lord YHWH!”

< Ezekiyel 31 >