< Ezekiyel 21 >
1 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
上主的話傳給我說:「
2 “Ɗan mutum, ka kafa fuskarka gāba da Urushalima ka kuma yi wa’azi a kan wuri mai tsarki. Ka yi annabci gāba da ƙasar Isra’ila
人子,你轉面向耶路撒冷,發言攻斥聖所,講預言攻斥以色列地域,
3 ka faɗa mata, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce ina gāba da ke. Zan ja takobina daga kubensa in karkashe adalai da mugaye daga cikinki.
向以色列地域說:吾主上主這樣說:看,我要攻擊你,我要拔劍出鞘,剷除你境內的義人和惡人,
4 Domin zan karkashe adalai da kuma mugaye, ba zan rufe takobina a kan kowa daga kudu zuwa arewa ba.
因為我要剷除你境內的義人和惡人,為此,我的劍從鞘內抽出,攻擊由南至北一切有血肉的人;
5 Sa’an nan duka mutane za su san cewa Ni Ubangiji na ja takobina daga kubensa; ba zai sāke koma kuma ba.’
這樣,凡有血肉的人都知道:是我,上主拔劍出鞘,決不再放回。
6 “Saboda ka yi nishi, ɗan mutum! Yi nishi a gabansu da ajiyar zuciya da ɓacin rai.
人子,你應哀歎! 應在他們眼前傷心痛苦哀歎。
7 Kuma sa’ad da suka tambaye ka, ‘Me ya sa kake nishi?’ Sai ka ce musu, ‘Domin labarun da suke fitowa. Kowace zuciya za tă narke kowane hannu kuma ya gurgunta; kowane ruhu zai sume kowane gwiwa kuma ta rasa ƙarfi kamar ruwa.’ Yana zuwa! Tabbatacce zai faru, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
假使有人問你說:你為什麼哀歎﹖你就說:是為了一個凶信,當這事來到,所有的心靈必要沮喪,手臂必要無力,精神必要頹唐,膝蓋必要軟弱如水。看,災禍來到時,必將如此──吾主上主的斷語。」
8 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
上主的話傳給我說:「
9 “Ɗan mutum, yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, “‘Takobi, takobi, wasasshe da kuma gogagge,
人子,講預言罷! 吾主這樣說:你要說:有一把劍:是一把磨快而擦亮的劍。
10 wasasshe don kisa, gogagge har yana walwal kamar walƙiya! “‘Kada ku yi farin ciki, hukunci yana zuwa, domin kowa ya ƙi jin abin da na yi gargaɗi a kai.
磨快了,是為大屠殺;擦亮了,是為閃爍發光。
11 “‘An ba da wannan takobi don a goge, don a kama da hannu; an washe shi aka kuma goge, shiryayye don a yi kisa da shi.
把它拿去擦亮,好握在掌中;這把磨快的劍,這把擦亮的劍,是為交在屠殺者的手中。
12 Ka yi kuka ka yi makoki, ɗan mutum, gama yana gāba da dukan sarakunan Isra’ila. An jefa su ga takobi tare da jama’ata. Saboda haka ku buga ƙirjinku.
人子,你要哀號痛哭,因為劍擊在我百姓身上,砍在以色列的一切首領身上。他們同我的百姓都喪身刀下。為此你應擊股示哀,
13 “‘Gwaji tabbatacce zai zo. Kuma a ce sandan Yahuda, wanda takobi ya ƙi, ya ci gaba? In ji Ubangiji Mai Iko Duka.’
因為已試過一次,這要怎麼辦﹖它連權杖都輕視了,以致不叫它存在──吾主上主的斷語──
14 “Saboda haka fa, ɗan mutum ka yi annabci ka kuma tafa hannuwanka. Bari takobi ya yi sara sau biyu, har sau uku ma. Takobin kisa ne, takobi ne don kisa mai girma, zai kewaye su a kowane gefe.
人子,你講預言,且鼓掌罷! 那劍將是雙刃的,是屠殺的劍;那把大屠殺的劍向他們揮起,
15 Domin zukata su narke da yawa kuma su fāɗi, na tsai da takobin kisa a dukan ƙofofinsu. Kash! A sa ya haska kamar walƙiya, ana riƙe da shi don kisa.
叫他們膽顫心驚,死亡的人加多。我將屠殺的劍尖指向他們所有的門戶上:劍擦亮了,是為閃爍;磨快了,是為屠殺。
16 Ya takobi, yi sara zuwa dama ka yi kuma zuwa hagu, duk inda aka juya ka.
你的刀鋒無論轉向何方,或向左,或向右,都應是鋒利的。
17 Zan tafa hannuwana, fushina kuwa zai sauka. Ni Ubangiji na faɗa.”
我也要親自鼓掌,以平息我的憤怒:這是我上主說的。」
18 Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
上主的話傳給我說:「
19 “Ɗan mutum, ka nuna hanyoyi biyu inda takobin sarkin Babilon zai bi, duka biyun su fara daga ƙasa guda. Ka kafa shaida inda hanyar za tă rabu zuwa cikin birni.
人子,你應劃出兩條路,叫巴比倫王的劍沿路而來。這兩條路應由一地出發;又劃出一隻手,置於通往城市的道路起點。
20 Ka nuna hanya guda wadda takobi zai fāɗo wa Rabba ta Ammonawa ɗayan kuma da zai fāɗo a kan Yahuda da kuma Urushalima mai katanga.
你所劃的路,一條使劍至阿孟子民的辣巴特;一條使劍至猶大的堅城耶路撒冷。
21 Gama sarkin Babilon zai tsaya a mararrabar hanya, a inda hanyar ta rabu biyu, don yă yi duba. Zai jefa ƙuri’a da kibiyoyinsa, zai nemi shawarar gumakansa, zai bincike hanta.
因為巴比倫王站在岔路上,在兩條路口上占卜、搖籤、求問「忒辣芬,」窺察牲肝。
22 A hannunsa na dama ƙuri’a don Urushalima za tă fito, inda zai kafa dundurusai, ya ba da umarni kisa, a yi kururuwar yaƙi, a kafa dundurusai a kan ƙofofi, a gina mahaurai a kuma yi ƙawanya.
在他右手中出現了指向耶路撒冷的籤,他便下令屠殺,吶喊衝鋒,架起攻城門機,堆起高台,建造雲梯。
23 Zai zama kamar duban ƙarya ne ga waɗanda suka yi rantsuwar yin masa biyayya, amma zai tunashe su game da laifinsu ya kuma kama su.
可是在曾經發過誓願的以色列子民看來,那籤是假的。但他卻想起了他們的罪過,為使他們俯首就擒。
24 “Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin ku mutanen nan kun tuna da laifinku ta wurin tawaye, kun kuma bayyana zunubanku cikin dukan abin da kuke yi, domin kun yi haka, za a kama ku.
為此吾主上主這樣說:因為你們顯露了你們的過犯,在你們的行為上,現出你們的惡行,使我想起了你們的罪惡;你們既然使我想起你們的罪惡,你們必在他們手中俯首就擒。
25 “‘Ya kai ƙazantaccen mugu, yerima Isra’ila, wanda kwanansa ta zo, wanda lokacin hukuncinsa ya cika fal,
你這無恥而萬惡的以色列首領,你的日子到了,犯罪的時候完了。
26 ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ka kunce rawanin, ka ɗauke rawanin nan. Ba zai zama kamar yadda yake ba. Za a ɗaukaka ƙasƙantacce, amma a ƙasƙantar da mai girma.
吾主上主這樣說:取下頭巾,摘去冠冕,一切都要轉變:卑下的要高陞,崇高的要降低。
27 Hallaka! Hallaka! Zan hallaka shi! Ba za a maido da shi ba sai ya ga ainihin mai shi; gare shi zan bayar da shi.’
我必要使他的國澈底滅亡,再也不能存在,直到那掌權者來到,我再交給他。」「
28 “Kai kuma, ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa game da Ammonawa da kuma zarginsu. “‘Takobi, takobi, an ja don kisa, an goge don cinyewa yana haske kamar walƙiya!
人子,你應講預言說,吾主上主這樣攻斥阿孟子民和他們的侮辱說:你要說:有一把劍,拔出是為屠殺,磨快是為毀滅,擦亮是為閃爍──
29 Duk da wahayin ƙarya game da kai, duban ƙarya game da kai, za a sa shi a wuyan mugaye waɗanda za a kashe, waɗanda kwanansu ta zo, waɗanda lokacin hukuncinsu ya cika fal.
那時人所給予你的,是虛假的異像,欺騙的占卜──是為砍在作惡犯罪者的脖子上,他們的日子到了,犯罪的時候完了。
30 “‘Ka mai da takobi a kubensa. A inda aka halicce ka, a ƙasar kakanninka, zan hukunta ka.
把劍插入鞘內,我要在你受造之地,在你生長之地裁判你。
31 Zan zub da hasalata a kanka in hura maka wutar fushina; Zan ba da kai a hannun mugayen mutanen da suka gwanince a hallakarwa.
我要在你身上發洩我的怒氣,在你身上點起我的怒火,將你交在善於破壞的野蠻人手中。
32 Za ka zama itacen wuta, za a zub da jininka a ƙasarka, ba za a ƙara tuna da kai ba; gama Ni Ubangiji na faɗa.’”
你要成為烈火的燃料;你的血要傾流在國中,以後再沒有人記念你,因為我上主說了。」