1Suka gina bagaden ƙona hadaya da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyar, fāɗinsa kamu biyar, murabba’i ke nan, tsayinsa kuwa kamu uku.
This chapter is missing in the source text.
2Suka yi ƙahoni a kusurwansa huɗu, ƙahonin da bagade a haɗe suke, suka kuma dalaye bagaden da tagulla.
3Da tagulla kuma ya yi duk kayayyakin bagaden, da kwanoni, da babban cokali, da daruna, da cokula masu yatsotsi, da farantan wuta.
4Suka yi wa bagaden raga, tagulla kuma don yă sa shi a tsakiya.
5Suka yi zubin zoban tagulla don riƙe sanduna a kusurwoyi huɗu na ragar tagullar.
6Suka yi sanduna da itacen ƙirya, suka kuma dalaye su da tagulla.
7Suka sa sandunan a cikin zoban saboda su kasance a gefen bagade don ɗaukarsa, suka yi rami cikinsa.
8Suka yi daro da gammonsa da tagulla daga madubai na mata masu yin aiki a ƙofar Tentin Sujada.
9Suka kuma yi filin Tentin Sujada. Suka yi labulanta na gefen kudu da lallausan lilin, tsawonsu kamu ɗari,
10da sanduna ashirin da rammukan sandunan tagulla ashirin, da kuma ƙugiyoyin azurfa da maɗauri a kan sandunan.
11Tsawon labule na wajen gefen arewa kamu ɗari ne, yana kuma da sanduna guda ashirin da rammuka ashirin na tagulla, da ƙugiyoyin azurfa da maɗaurai a kan sandunan.
12Labule na gefen yamma kamu hamsin, da sanduna guda goma, da rammuka guda goma, da ƙugiyoyin azurfa da maɗaurai a kan sandunan.
13A ƙarshen gefen gabas, wajen fitowar rana, shi ma fāɗinsa kamu hamsin ne.
14Labule na gefe ɗaya na ƙofar, kamu goma sha biyar ne, da sanduna guda uku da rammukansu,
15akwai labule mai kamu goma sha biyar a ɗayan gefen ƙofar shiga zuwa filin Tentin Sujada, da sanduna uku da rammuka uku.
16An yi dukan labulan da suke kewaye da filin Tentin Sujada da lallausan zaren lilin.
17An yi rammukan sandunan da tagulla. An dalaye ƙugiyoyi da maɗauran da suke kan sandunan da azurfa; saboda haka dukan sandunan filin Tentin Sujada suna da maɗaurai na azurfa.
18Aka yi wa labulen ƙofar filin Tentin Sujada ado na ɗinki da na shuɗi, da na shunayya, da na jan zare, da na lallausan lilin, aikin gwaninta. Tsawonsa kamu ashirin, kuma kamar yadda labulen filin Tentin Sujada suke, tsayinsa kamu biyar ne,
19da sanduna guda huɗu da rammuka guda huɗu na tagulla. Ƙugiyoyinsu da maɗauransu na azurfa ne, aka kuma dalaye bisansu da azurfa.
20Aka yi dukan ƙarafan kafa tabanakul da kuma na kewayen filin Tentin Sujada da tagulla ne.
21Waɗannan su ne kayayyakin da aka yi amfani da su domin aikin tabanakul, da tabanakul na Shaida, waɗanda aka rubuta bisa ga umarnin Musa ta wurin Lawiyawa, a ƙarƙashin jagorancin Itamar ɗan Haruna, firist.
22(Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuda, ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa;
23tare da shi akwai Oholiyab ɗan Ahisamak, na kabilar Dan, shi gwani ne cikin aikin zāne-zāne, da ɗinki na shuɗi, da na shunayya, da na jan zare, da na lallausan lilin.)
24Jimillar zinariya daga hadaya ta kaɗawar da aka yi amfani da su domin aikin wuri mai tsarki ta kai talenti 29 da shekel 730, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri.
25Azurfar da aka samu daga ƙidayar taron jama’a, talenti 100 ne, da shekel 1,775, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri.
26Duk mutumin da ya shiga ƙirge daga mai shekaru ashirin zuwa gaba, ya ba da rabin shekel. Mazan da suka shiga ƙirge sun kai mutum 603,550.
27An yi amfani da azurfa talenti 100 don yin rammuka na wuri mai tsarki, da kuma rammukan labule, rammuka 100 daga talenti 100, talenti ɗaya don rami ɗaya.
28Suka yi amfani da shekel 1,775 don yin ƙugiyoyi saboda sanduna, suka dalaye bisan sandunan da maɗauransu.
29Tagullar da aka bayar daga hadaya ta kaɗawa ya kai talenti 70 da shekel 2,400.
30Suka yi amfani da shi don yin rammukan ƙofar Tentin Sujada, da bagaden tagulla tare da ragar tagulla da dukan kayayyakinsa,
31da rammukan sanduna don kewaye filin, da waɗanda suke ƙofarsa, da dukan ƙarafan kafa tenti don tabanakul, da kuma don kewaye filin.