< Fitowa 15 >

1 Sa’an nan Musa da Isra’ilawa suka rera wannan waƙa ga Ubangiji suka ce, “Zan rera waƙa ga Ubangiji gama an ɗaukaka shi ƙwarai. Doki da mahayinsa ya jefa su cikin teku.
那时,摩西和以色列人向耶和华唱歌说: 我要向耶和华歌唱,因他大大战胜, 将马和骑马的投在海中。
2 “Ubangiji ne ƙarfina da mafakata, ya zama cetona. Shi Allahna ne, zan yabe shi. Allah na kakana, zan ɗaukaka shi.
耶和华是我的力量,我的诗歌, 也成了我的拯救。 这是我的 神,我要赞美他, 是我父亲的 神,我要尊崇他。
3 Ubangiji mai yaƙi ne Ubangiji ne sunansa.
耶和华是战士; 他的名是耶和华。
4 Karusan Fir’auna da sojojinsa ya jefa cikin teku. Zaɓaɓɓun jarumawansa ya nutsar da su cikin Bahar Maliya.
法老的车辆、军兵,耶和华已抛在海中; 他特选的军长都沉于红海。
5 Zurfafan ruwaye sun rufe su; suka nutse cikin zurfi kamar dutse.
深水淹没他们; 他们如同石头坠到深处。
6 Hannun damanka, ya Ubangiji, Mai kwarjini ne da iko, hannun damanka, ya Ubangiji, ya farfashe magabci.
耶和华啊,你的右手施展能力,显出荣耀; 耶和华啊,你的右手摔碎仇敌。
7 “A cikin girman kwarjininka ka kā da waɗanda sun yi gāba da kai. Ka aiki fushinka mai zafi ya cinye su kamar tattaka.
你大发威严,推翻那些起来攻击你的; 你发出烈怒如火,烧灭他们像烧碎秸一样。
8 Da hucin numfashin hancinka ruwaye suka tattaru. Ruwaye masu kwararowa, suka tsaya kamar bango; ruwaye na zurfafa suka daskare a tsakiyar teku.
你发鼻中的气,水便聚起成堆, 大水直立如垒, 海中的深水凝结。
9 Magabci ya yi fahariya, cewa ‘Zan fafare su, in ci musu. Zan raba ganima; abin da na so ya samu. Zan ja takobina hannuna kuwa zai hallaka su.’
仇敌说:我要追赶,我要追上; 我要分掳物,我要在他们身上称我的心愿。 我要拔出刀来,亲手杀灭他们。
10 Amma ka hura numfashinka sai teku ya rufe su. Suka nutse kamar darma cikin manyan ruwaye.
你叫风一吹,海就把他们淹没; 他们如铅沉在大水之中。
11 Wane ne cikin alloli, ya yi kamar ka, ya Ubangiji? Wane ne kamar ka, mai ɗaukaka cikin tsarki, mai banrazana cikin ɗaukaka, mai aikata al’ajabai?
耶和华啊,众神之中,谁能像你? 谁能像你—至圣至荣, 可颂可畏,施行奇事?
12 “Ka miƙa hannunka na dama, ƙasa ta haɗiye abokan gābanka.
你伸出右手, 地便吞灭他们。
13 A cikin ƙaunarka marar iyaka, za ka bishe mutanen da ka fansa. A cikin ƙarfinka, za ka bishe su zuwa mazauninka mai tsarki.
你凭慈爱领了你所赎的百姓; 你凭能力引他们到了你的圣所。
14 Al’ummai za su ji, su yi rawar jiki tsoro zai kama mutanen Filistiya.
外邦人听见就发颤; 疼痛抓住非利士的居民。
15 Sarakunan Edom za su tsorata, shugabannin Mowab za su yi rawar jiki, mutanen Kan’ana za su narke.
那时,以东的族长惊惶, 摩押的英雄被战兢抓住, 迦南的居民心都消化了。
16 Razana da tsoro za su fāɗo a kansu. Da ikon hannunka za su tsaya cik kamar dutse, har sai mutanen da ka kawo sun wuce, ya Ubangiji.
惊骇恐惧临到他们。 耶和华啊,因你膀臂的大能, 他们如石头寂然不动, 等候你的百姓过去, 等候你所赎的百姓过去。
17 Za ka kawo su, ka dasa su a kan dutsen nan naka inda, ya Ubangiji, ka shirya domin mazauninka, wuri mai tsarkin da hannuwanka suka kafa, ya Ubangiji.
你要将他们领进去,栽于你产业的山上— 耶和华啊,就是你为自己所造的住处; 主啊,就是你手所建立的圣所。
18 “Ubangiji zai yi mulki har abada abadin.”
耶和华必作王,直到永永远远!
19 Sa’ad da dawakai, kekunan yaƙi da mahayan dawakan Fir’auna suka shiga cikin teku, Ubangiji ya mayar da ruwan teku a kansu, amma Isra’ilawa suka wuce a cikin teku a busasshiyar ƙasa.
法老的马匹、车辆,和马兵下到海中,耶和华使海水回流,淹没他们;惟有以色列人在海中走干地。
20 Sa’an nan Miriyam annabiya,’yar’uwar Haruna ta ɗauki ganga a hannunta, dukan mata kuwa suka bi ta, da ganguna suna rawa.
亚伦的姊姊,女先知米利暗,手里拿着鼓;众妇女也跟她出去拿鼓跳舞。
21 Miriyam ta yi musu waƙa. “Ku rera ga Ubangiji gama ya ci gawurtacciyar nasara. Doki da mahayi, ya jefa cikin teku.”
米利暗应声说: 你们要歌颂耶和华,因他大大战胜, 将马和骑马的投在海中。
22 Sai Musa ya jagoranci Isra’ila daga jan teku zuwa hamadar Shur. Kwana uku suka yi tafiya cikin hamada ba su sami ruwa ba.
摩西领以色列人从红海往前行,到了书珥的旷野,在旷野走了三天,找不着水。
23 Da suka zo Mara, ba su iya shan ruwan ba saboda yana da ɗaci (shi ya sa ake kira wurin Mara).
到了玛拉,不能喝那里的水;因为水苦,所以那地名叫玛拉。
24 Sai mutanen suka yi gunaguni a kan Musa, suna cewa, “Me za mu sha?”
百姓就向摩西发怨言,说:“我们喝什么呢?”
25 Sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya nuna masa wani itace. Sai ya jefa shi cikin ruwan, sai ruwan ya zama mai daɗi. A can Ubangiji ya yi musu doka da farilla, a can kuma ya gwada su.
摩西呼求耶和华,耶和华指示他一棵树。他把树丢在水里,水就变甜了。 耶和华在那里为他们定了律例、典章,在那里试验他们;
26 Ya ce, “In kun kasa kunne ga muryar Ubangiji Allahnku kuka yi abin da yake daidai a idanunsa, in kun mai da hankali ga umarnansa, kuka kiyaye dukan farillansa, ba zan kawo muku wani ciwon da na kawo a kan Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji da nake warkar da ku.”
又说:“你若留意听耶和华—你 神的话,又行我眼中看为正的事,留心听我的诫命,守我一切的律例,我就不将所加与埃及人的疾病加在你身上,因为我—耶和华是医治你的。”
27 Sai suka zo Elim inda akwai maɓulɓulan ruwa goma sha biyu da itatuwan dabino saba’in, suka sauka a can, kusa da ruwa.
他们到了以琳,在那里有十二股水泉,七十棵棕树;他们就在那里的水边安营。

< Fitowa 15 >