< Ayyukan Manzanni 21 >

1 Bayan muka rabu da su da ƙyar, sai muka shiga jirgin ruwa, muka miƙe zuwa Kos. Kashegari muka tafi Rods daga can kuma muka je Fatara.
When at least we had torn ourselves away, and had set sail, we ran a straight course to Cos, and next day to Rhodes, and from there to Patara.
2 Sai muka sami wani jirgin ruwa da zai ƙetare zuwa Funisiya, sai muka shiga muka kama tafiya.
And when we had found a ship bound for Phoenicia, we went aboard and set sail.
3 Bayan muka hangi Saifurus muka wuce shi ta kudu, sai muka ci gaba zuwa Suriya. Muka sauka a Taya, inda jirgin ruwanmu zai sauke kayansa.
After sighting Cyprus and leaving it on the left hand, we sailed for Syria, and put in at Tyre; for there the ship was to unload her cargo.
4 Da muka sami almajirai a can, sai muka zauna da su kwana bakwai. Ta wurin Ruhu, suka yi ƙoƙari su hana Bulus wucewa zuwa Urushalima.
We looked up the local disciples and remained there seven days; and these disciples kept telling Paul, through the Spirit, that he should not set foot in Jerusalem.
5 Amma da lokacin tashinmu ya yi, sai muka tashi muka ci gaba da tafiyarmu. Dukan almajirai da matansu da’ya’yansu suka raka mu har bayan birni, a can kuwa a bakin teku muka durƙusa muka yi addu’a.
When, however, our time was up, we left and started on our journey; and all of them, with wives and children, were escorting us on our way until we were out of the city; then, kneeling down on the beach, we prayed,
6 Bayan mun yi bankwana da juna, sai muka shiga jirgin ruwa, su kuwa suka koma gida.
and said good-bye, and went on board the ship, while they returned home again.
7 Muka ci gaba da tafiyarmu daga Taya muka sauka a Tolemayis, inda muka gai da’yan’uwa muka yi kwana ɗaya tare da su.
And when we had finished the voyage from Tyre, we reached Ptolemais, and greeted the brothers and stayed with them one day.
8 Da muka tashi kashegari, sai muka isa Kaisariya muka kuma sauka a gidan Filibus mai bishara, ɗaya daga cikin Bakwai ɗin nan.
On the morrow we started for Caesarea, where we went into the house of Philip, the evangelist, who was one of the seven, and stayed with him.
9 Yana da’ya’ya huɗu’yan mata da ba su yi aure ba, waɗanda suka yi annabci.
Now Philip had four unmarried daughters who prophesied,
10 Bayan muka yi’yan kwanaki da dama a can, sai wani annabin da ake kira Agabus ya gangaro daga Yahudiya.
and while we remained there many days, a prophet named Agabus came down from Judea.
11 Da ya zo wurinmu, sai ya ɗauki ɗamarar Bulus, ya ɗaura hannuwansa da ƙafafunsa da ita sa’an nan ya ce, “Ruhu Mai Tsarki ya ce, ‘Haka Yahudawan Urushalima za su daure mai wannan ɗamara su kuma ba da shi ga Al’ummai.’”
He came to us, and taking Paul’s girdle, he bound his own feet and hands, saying, "Thus says the Holy Spirit, ‘so will the Jews at Jerusalem bind the owner of this girdle, and deliver him into the hands of the Gentiles.’"
12 Sa’ad da muka ji haka, sai mu da mutanen da suke can muka roƙi Bulus kada yă je Urushalima.
As soon as we heard these words, both we and those who were standing near entreated Paul not to go up to Jerusalem.
13 Sai Bulus ya amsa ya ce, “Don me kuke kuka kuna kuma ɓata mini zuciya? A shirye nake ba ma a daure ni kawai ba, amma har ma in mutu a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.”
"What do you mean by thus breaking my heart with your grief?" answered Paul. "For I am ready not to be bound only, but also to die at Jerusalem, for the name of the Lord Jesus."
14 Da dai ya ƙi rarrasuwa, muka yi shiru, muka ce, “Bari Ubangiji yă yi nufinsa.”
And when he would not be persuaded, we ceased, saying, "The will of the Lord be done."
15 Bayan haka, sai muka shirya muka kuma haura zuwa Urushalima.
A few days after this we took up our luggage and went up to Jerusalem.
16 Waɗansu almajirai daga Kaisariya suka raka mu suka kawo mu gidan Minason, inda za mu sauka. Shi mutumin Saifurus ne kuma ɗaya daga cikin almajirai na farko.
And some of the disciples from Caesarea accompanied us. They led us to the house of Mnason, a Cypriote, a disciple of long standing, with whom we were to lodge.
17 Sa’ad da muka zo Urushalima,’yan’uwa suka karɓe mu da murna.
At length we reached Jerusalem, and the brothers there received us gladly.
18 Kashegari Bulus da sauranmu muka tafi domin mu ga Yaƙub, dukan dattawan kuwa suna nan.
On the following day we went with Paul to call on James, and all the elders were present.
19 Bulus ya gaishe su ya kuma ba su rahoto dalla-dalla a kan abin da Allah ya yi a cikin Al’ummai ta wurin aikinsa.
After saluting them Paul rehearsed, one by one, the things that God had done among the Gentiles by his ministry.
20 Da suka ji haka, sai suka yabi Allah. Sa’an nan suka ce wa Bulus, “Ka gani ɗan’uwa, yawan dubban Yahudawan da suka gaskata, kuma dukansu masu himma ne a wajen bin doka.
And they, when they heard it, glorified God, and said to him. "You see, brother, how many thousands there are among the Jews, of those who have believed, and they are all zealous for the Law.
21 An sanar da su cewa kana koya wa dukan Yahudawan da suke zama a cikin Al’ummai cewa su juye daga Musa, kana kuma faɗa musu kada su yi wa’ya’yansu kaciya ko su yi rayuwa bisa ga al’adunmu.
"Now what they have been told about you, again and again, is that you teach all the Jews who are among the Gentiles, to forsake Moses, and not to circumcise their children, nor to follow the old customs.
22 To, me za mu yi ke nan? Lalle za su ji cewa ka iso,
"What then ought to be done? They will certainly hear that you are come.
23 saboda haka, ka yi abin da muka faɗa maka. Akwai mutum huɗu tare da mu da suka yi alkawari.
"So do this that we tell you.
24 Ka ɗauki waɗannan mutane, ka tafi da su ku tsarkaka gaba ɗaya, ka kuma biya musu kome don su samu su yi aski. Ta haka kowa zai sani babu gaskiya a waɗannan rahotanni game da kai, za a kuma ga cewa kai kanka kana kiyaye dokar.
"We have four men here under a vow; associate yourself with them, purify yourself with them, and pay their expenses so that they may have their heads shaved; then every one will know that there is no truth in the rumors that they have heard about you; but that you yourself walk orderly obeying the law.
25 Game da Al’ummai masu bi kuwa, mun yi musu wasiƙa a kan shawararmu cewa su guji abincin da aka miƙa wa gumaka, da jini, da naman dabbar da aka maƙure da kuma fasikanci.”
"As for the Gentile believers, we wrote giving judgment that they should abstain from anything sacrificed to an idol, from blood, from what is strangled, and from fornication."
26 Kashegari, sai Bulus ya ɗauki mutanen ya kuma tsarkake kansa tare da su. Sa’an nan ya tafi haikali domin yă sanar da ranar cikar tsarkakewarsu da kuma ranar da za a ba da sadaka domin kowannensu.
Then Paul took the men, and after purifying himself with them next day, went into the temple to declare the fulfilment of the days of purification, until the offering was offered for every one of them.
27 Da kwana bakwai ɗin suka yi kusan cika, waɗansu Yahudawa daga lardin Asiya suka ga Bulus a haikali. Sai suka zuga taron duka, suka kama shi,
But when the seven days were almost over, the Asiatic Jews caught sight of him in the temple, and began to stir up all the crowd, and laid hands on him, shouting.
28 suna ihu suna cewa “Mutanen Isra’ila ku taimake mu! Ga mutumin da yake koya wa dukan mutane ko’ina cewa su ƙi mutanenmu da dokarmu da kuma wannan wuri. Ban da haka ma, ya kawo Hellenawa a cikin filin haikali ya ƙazantar da wurin nan mai tsarki.”
"Men of Israel, help! This is the man who goes everywhere preaching to everybody against the people, and the Law, and this place. And he has actually brought Gentiles even into the temple, and has desecrated the holy place."
29 (Dā ma can sun ga Turofimus mutumin Afisa a birni tare da Bulus suka yi tsammani Bulus ya kawo shi filin haikali.)
(For they had formerly seen Trophimus, the Ephesian, with him in the city, and supposed that Paul had brought him into the temple.)
30 Duk birnin ya ruɗe, mutane suka zaburo da gudu daga kowane gefe. Suka kama Bulus, suka ja shi daga haikali, nan da nan aka rurrufe ƙofofi.
The whole city was thrown into uproar. The mob surged together, seized Paul, and began to drag him outside the temple. Whereupon the doors were at once shut.
31 Yayinda suke ƙoƙari su kashe shi, sai labari ya kai ga shugaban ƙungiyar sojan Roma cewa birnin Urushalima duk ta hargitse.
While they were attempting to kill him, news came to the tribune commander of the garrison that all Jerusalem was in an uproar.
32 Nan da nan ya ɗibi waɗansu hafsoshi da sojoji suka gangara a guje wurin taron. Da masu hargitsin suka ga shugaban ƙungiyar sojan da sojojinsa, sai suka daina dūkan Bulus.
At once he took soldiers and centurions, and rushed down upon them. When they saw the tribune and the troops, they left off beating Paul.
33 Shugaban ƙungiyar sojan ya zo ya kama shi ya ba da umarni a daure shi da sarƙoƙi biyu. Sa’an nan ya yi tambaya ko shi wane ne, da kuma abin da ya yi.
Then the tribune came up and seized him, and ordered that he be bound with two chains. "Who is he?" he began asking, "and what has he done?"
34 Waɗansu daga cikin taron suka ɗau kururuwa suna ce abu kaza, waɗansu kuma suna ce abu kaza, da yake shugaban ƙungiyar sojan ya kāsa samun ainihin tushen maganar saboda yawan hayaniyar, sai ya yi umarni a kai Bulus barikin soja.
Some among the crowd kept shouting one thing, some another; and when the tribune could not learn the facts because of the uproar, he ordered Paul into the barracks.
35 Sa’ad da Bulus ya kai bakin matakala, sai da sojoji suka ɗaga shi sama saboda tsananin haukan taron.
When was going up the steps, he had to be carried by the soldiers, because of the violence of the mob,
36 Taron da suka bi suka dinga kururuwa, suna cewa, “A yi da shi!”
for the whole mass of the people were following him, shouting, "Away with him!"
37 Da sojoji suka kai gab da shigar da Bulus cikin bariki, sai ya ce wa shugaban ƙungiyar sojan, “Ko ka yarda in yi magana da kai?” Sai ya amsa ya ce, “Ka iya Girik ne?
Just as he was about to be taken into the barracks, Paul said to the tribune, "May I speak to you?"
38 Ba kai ba ne mutumin Masar nan da ya haddasa tawaye har ya yi jagorar’yan ta’ada dubu huɗu zuwa hamada a shekarun baya?”
"Do you know Greek?" said the tribune; "Are you not, then, the Egyptian who in days gone by stirred up to sedition, and let into the wilderness the four thousand cutthroats?"
39 Bulus ya amsa ya ce, “Ni mutumin Yahuda ne, daga Tarshish a Silisiya shahararren birnin nan. In ka yarda bari in yi wa mutane magana.”
"I am a Jew," answered Paul, "a native of Tarsus in Cilicia, a citizen of no mean city. And I pray you, give me permission to speak to the people."
40 Da ya sami izini daga shugaban ƙungiyar sojan, sai Bulus ya tsaya a matakala, ya ɗaga wa taron hannu. Da dukan suka yi shiru, sai ya ce musu da Arameyanci,
So when he had given leave, Paul stood on the stairs, beckoning with his hands to the people. There came a great hush, and he spoke to them as follows, in Hebrew.

< Ayyukan Manzanni 21 >