< 2 Sama’ila 22 >

1 Dawuda ya rera wannan waƙa ga Ubangiji, sa’ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun dukan abokan gābansa, da kuma daga hannun Shawulu.
当耶和华救大卫脱离一切仇敌和扫罗之手的日子,他向耶和华念这诗,
2 Ya ce, “Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona;
说: 耶和华是我的岩石, 我的山寨,我的救主,
3 Allahna shi ne dutsena. A gare shi nake samun kāriya shi ne garkuwata da kuma ƙahon cetona. Shi ne mafakata, maɓuyata, da mai cetona. Daga mutane masu fitina, ka cece ni.
我的 神,我的磐石,我所投靠的。 他是我的盾牌,是拯救我的角, 是我的高台,是我的避难所。 我的救主啊,你是救我脱离强暴的。
4 “Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo, na kuwa tsira daga abokan gābana.
我要求告当赞美的耶和华, 这样,我必从仇敌手中被救出来。
5 Raƙumar ruwan mutuwa sun kewaye ni; raƙumar ruwan hallaka suna cin ƙarfina.
曾有死亡的波浪环绕我, 匪类的急流使我惊惧,
6 Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe ni; tarkuna kuma suka auka mini. (Sheol h7585)
阴间的绳索缠绕我, 死亡的网罗临到我。 (Sheol h7585)
7 “A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji; na yi kira ga Allahna. Daga cikin haikalinsa ya saurare muryata; kukata ta zo kunnensa.
我在急难中求告耶和华, 向我的 神呼求。 他从殿中听了我的声音; 我的呼求入了他的耳中。
8 Ƙasa ta yi rawa ta kuma girgiza, harsashan sararin sama sun jijjigu; suka yi makyarkyata saboda yana fushi.
那时因他发怒,地就摇撼战抖; 天的根基也震动摇撼。
9 Hayaƙi ya taso daga kafaffen hancinsa; harshen wuta mai cinyewa daga bakinsa, garwashi mai ƙuna daga bakinsa.
从他鼻孔冒烟上腾; 从他口中发火焚烧,连炭也着了。
10 Ya buɗe sararin sama, ya sauko ƙasa, girgije mai duhu suna ƙarƙashin ƙafafunsa.
他又使天下垂,亲自降临; 有黑云在他脚下。
11 Ya hau kerubobi, ya tashi sama; ya yi firiya a fikafikan iska.
他坐着基路伯飞行, 在风的翅膀上显现。
12 Ya mai da duhu abin rufuwarsa gizagizai masu kauri cike da ruwa suka kewaye shi.
他以黑暗和聚集的水、 天空的厚云为他四围的行宫。
13 Daga cikin hasken gabansa garwashi wuta mai ci ya yi walƙiya.
因他面前的光辉炭都着了。
14 Ubangiji ya yi tsawa daga sararin sama; aka ji muryar Mafi Ɗaukaka.
耶和华从天上打雷; 至高者发出声音。
15 Ya harbe kibiyoyi, ya wartsar da abokan gāba, da walƙiya kuma ya sa suka gudu.
他射出箭来,使仇敌四散, 发出闪电,使他们扰乱。
16 Aka bayyana kwarin teku, tushen duniya suka tonu. A tsawatawar Ubangiji, da numfashinsa mai ƙarfi daga hancinsa.
耶和华的斥责一发,鼻孔的气一出, 海底就出现,大地的根基也显露。
17 “Daga sama ya miƙo hannu ya ɗauke ni, ya tsamo ni daga zurfafa ruwaye.
他从高天伸手抓住我, 把我从大水中拉上来。
18 Ya kuɓutar da ni daga hannun abokin gāba mai iko, daga maƙiyina da suka fi ƙarfina.
他救我脱离我的劲敌和那些恨我的人, 因为他们比我强盛。
19 Suka auka mini cikin ranar masifata, amma Ubangiji ya kiyaye ni.
我遭遇灾难的日子,他们来攻击我; 但耶和华是我的倚靠。
20 Ya fito da ni, ya kai ni wuri mafi fāɗi; ya kuɓutar da ni gama yana jin daɗina.
他又领我到宽阔之处; 他救拔我,因他喜悦我。
21 “Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina; bisa ga tsabtar hannuwana ya sāka mini.
耶和华按着我的公义报答我, 按着我手中的清洁赏赐我。
22 Gama na kiyaye hanyoyin Ubangiji; ban yi wani mugun abu da zai juyar da ni daga Allahna ba.
因为我遵守了耶和华的道, 未曾作恶离开我的 神。
23 Dukan dokokinsa suna a gabana; ban ƙi ko ɗaya daga umarnansa ba.
他的一切典章常在我面前; 他的律例,我也未曾离弃。
24 Ba ni da laifi a gabansa na kiyaye kaina daga yin zunubi.
我在他面前作了完全人; 我也保守自己远离我的罪孽。
25 Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina bisa ga tsarkina a gabansa.
所以耶和华按我的公义, 按我在他眼前的清洁赏赐我。
26 “Ga masu aminci, kakan nuna kanka mai aminci, ga marasa laifi, kakan nuna kanka marar laifi,
慈爱的人,你以慈爱待他; 完全的人,你以完全待他;
27 ga masu tsarki, kakan nuna musu tsarki. Amma ga masu karkataccen hali, kakan nuna kanka mai wayo.
清洁的人,你以清洁待他; 乖僻的人,你以弯曲待他。
28 Kakan ceci mai tawali’u, amma idanunka suna a kan masu girman kai don ka ƙasƙantar da su.
困苦的百姓,你必拯救; 但你的眼目察看高傲的人,使他降卑。
29 Ya Ubangiji kai ne fitilata; Ubangiji ya mai da duhuna haske.
耶和华啊,你是我的灯; 耶和华必照明我的黑暗。
30 Da taimakonka zan iya auka wa rundunar sojoji; tare da Allahna zan iya hawan katanga.
我借着你冲入敌军, 借着我的 神跳过墙垣。
31 “Ga Allah dai, hanyarsa cikakkiya ce; maganar Ubangiji babu kuskure. Shi garkuwa ce ga waɗanda suka nemi mafaka a gare shi.
至于 神,他的道是完全的; 耶和华的话是炼净的。 凡投靠他的,他便作他们的盾牌。
32 Gama wane ne Allah, in ba Ubangiji ba? Wane ne dutse kuma in ba Allahnmu ba?
除了耶和华,谁是 神呢? 除了我们的 神,谁是磐石呢?
33 Allah ne ya ba ni ƙarfi, ya kuma mai da hanyata cikakkiya.
神是我坚固的保障; 他引导完全人行他的路。
34 Ya sa ƙafafuna kamar ƙafafun barewa; ya sa na iya tsayawa a kan duwatsu.
他使我的脚快如母鹿的蹄, 又使我在高处安稳。
35 Ya hori hannuwana don yaƙi, hannuwana za su iya tanƙware bakan tagulla.
他教导我的手能以争战, 甚至我的膀臂能开铜弓。
36 Ka ba ni garkuwar nasararka; ka sauko don ka sa in sami girma.
你把你的救恩给我作盾牌; 你的温和使我为大。
37 Ka fadada hanya a ƙarƙashina domin kada idon ƙafana yă juya.
你使我脚下的地步宽阔; 我的脚未曾滑跌。
38 “Na fafari abokan gābana, na murƙushe su; ban kuwa juya ba sai da na hallaka su.
我追赶我的仇敌,灭绝了他们, 未灭以先,我没有归回。
39 Na hallaka su ƙaƙaf, ba kuwa za su ƙara tashi ba, sun fāɗi a ƙarƙashin sawuna.
我灭绝了他们, 打伤了他们,使他们不能起来; 他们都倒在我的脚下。
40 Ka ba ni ƙarfi don yaƙi; ka sa maƙiyina suka rusuna a ƙafafuna.
因为你曾以力量束我的腰,使我能争战; 你也使那起来攻击我的都服在我以下。
41 Ka sa abokan gābana suka juya a guje, na kuwa hallaka maƙiyina.
你又使我的仇敌在我面前转背逃跑, 叫我能以剪除那恨我的人。
42 Suka nemi taimako, amma babu wanda zai cece su, suka yi kira ga Ubangiji, amma ba a amsa musu ba.
他们仰望,却无人拯救; 就是呼求耶和华,他也不应允。
43 Na murƙushe su, suka yi laushi kamar ƙura; na daka na kuma tattake su kamar caɓi a kan tituna.
我捣碎他们,如同地上的灰尘, 践踏他们,四散在地,如同街上的泥土。
44 “Ka kuɓutar da ni daga harin mutanena; ka kiyaye ni kamar shugaban al’ummai. Mutanen da ban sansu ba za su kasance a ƙarƙashina,
你救我脱离我百姓的争竞, 保护我作列国的元首; 我素不认识的民必事奉我。
45 baƙi kuma su na zuwa don su yi mini fadanci; da zarar sun ji ni, sukan yi mini biyayya.
外邦人要投降我, 一听见我的名声就必顺从我。
46 Zukatansu ta karaya; suka fito da rawan jiki daga kagararsu.
外邦人要衰残, 战战兢兢地出他们的营寨。
47 “Ubangiji yana a raye! Yabo ta tabbata ga Dutsena! Ɗaukaka ga Allah, Dutse, Mai Cetona!
耶和华是活神,愿我的磐石被人称颂! 愿 神—那拯救我的磐石被人尊崇!
48 Shi ne Allahn da yake rama mini, wanda ya sa al’ummai a ƙarƙashina,
这位 神就是那为我伸冤、 使众民服在我以下的。
49 wanda ya kuɓutar da ni daga maƙiyina. Ka ɗaukaka ni bisa maƙiyina; ka kiyaye ni daga hannun mugayen mutane.
你救我脱离仇敌, 又把我举起,高过那些起来攻击我的; 你救我脱离强暴的人。
50 Saboda haka, zan yabe ka, ya Ubangiji cikin dukan al’ummai; Zan rera waƙoƙin yabo ga sunanka.
耶和华啊,因此我要在外邦中称谢你, 歌颂你的名。
51 “Ya ba wa sarkinsa kyakkyawan nasara; ya nuna madawwamiyar ƙauna ga shafaffensa, ga Dawuda da zuriyarsa har abada.”
耶和华赐极大的救恩给他所立的王, 施慈爱给他的受膏者, 就是给大卫和他的后裔, 直到永远!

< 2 Sama’ila 22 >