< 2 Tarihi 1 >
1 Solomon ɗan Dawuda ya kafa kansa sosai a bisa masarautarsa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi ya kuma sa ya zama mai girma sosai.
confortatus est ergo Salomon filius David in regno suo et Dominus erat cum eo et magnificavit eum in excelsum
2 Sai Solomon ya yi magana ga dukan Isra’ila, ga shugabannin mayaƙa dubu-dubu da shugabannin mayaƙa ɗari-ɗari, ga alƙalai da kuma ga dukan shugabanni a Isra’ila, kawunan iyalai,
praecepitque Salomon universo Israheli tribunis et centurionibus et ducibus et iudicibus omnis Israhel et principibus familiarum
3 Solomon tare da dukan taron suka tafi masujadan kan tudu a Gibeyon, gama Tentin Sujadar Allah yana can, wanda Musa bawan Ubangiji ya yi a hamada.
et abiit cum universa multitudine in excelsum Gabaon ubi erat tabernaculum foederis Dei quod fecit Moses famulus Dei in solitudine
4 Dawuda ya riga ya haura da akwatin alkawarin Allah daga Kiriyat Yeyarim zuwa inda ya shirya dominsa, domin yă kafa masa tenti a Urushalima.
arcam autem Dei adduxerat David de Cariathiarim in locum quem paraverat ei et ubi fixerat illi tabernaculum hoc est in Hierusalem
5 Amma bagaden tagullar da Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, ya yi a Gibeyon a gaba tabanakul na Ubangiji; saboda haka Solomon da taron suka neme nufin Ubangiji a can.
altare quoque aeneum quod fabricatus fuerat Beselehel filius Uri filii Ur ibi erat coram tabernaculo Domini quod et requisivit Salomon et omnis ecclesia
6 Solomon ya haura zuwa bagaden tagulla a gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada, ya kuma miƙa hadayu na ƙonawa dubbai a kansa.
ascenditque Salomon ad altare aeneum coram tabernaculo foederis Domini et obtulit in eo mille hostias
7 A wannan dare Allah ya bayyana ga Solomon, ya ce masa, “Roƙi duk abin da kake so in ba ka.”
ecce autem in ipsa nocte apparuit ei Deus dicens postula quod vis ut dem tibi
8 Solomon ya amsa wa Allah, “Ka nuna alheri mai girma ga Dawuda mahaifina ka kuma naɗa ni sarki a matsayinsa.
dixitque Salomon Deo tu fecisti cum David patre meo misericordiam magnam et constituisti me regem pro eo
9 To, yanzu, ya Ubangiji Allah, ka cika alkawarin da ka yi ga mahaifina Dawuda yă tabbata, gama ka naɗa ni sarki a bisa mutanen da suka wuce ƙirge kamar ƙurar ƙasa.
nunc igitur Domine Deus impleatur sermo tuus quem pollicitus es David patri meo tu enim fecisti me regem super populum tuum multum qui tam innumerabilis est quam pulvis terrae
10 Ka ba ni hikima da sani, don in iya jagorance wannan mutane, gama wa zai iya shugabance wannan jama’arka mai girma?”
da mihi sapientiam et intellegentiam ut egrediar coram populo tuo et ingrediar quis enim potest hunc populum tuum digne qui tam grandis est iudicare
11 Allah ya ce wa Solomon, “Da yake wannan ne sha’awar zuciyarka, ba ka kuwa nemi wadata, arziki ko girma ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, da yake kuma ba ka nemi tsawon rai ba, amma ka nemi hikima da sani don ka shugabanci jama’ata wadda na naɗa ka sarki,
dixit autem Deus ad Salomonem quia hoc magis placuit cordi tuo et non postulasti divitias et substantiam et gloriam neque animas eorum qui te oderunt sed nec dies vitae plurimos petisti autem sapientiam et scientiam ut iudicare possis populum meum super quem constitui te regem
12 saboda haka za a ba ka hikima da sani. Zan kuma ba ka wadata, arziki da girma, waɗanda babu wani sarki kafin kai da ya taɓa kasance da su kuma babu wani a bayanka da zai kasance da su.”
sapientia et scientia data sunt tibi divitias autem et substantiam et gloriam dabo tibi ita ut nullus in regibus nec ante te nec post te fuerit similis tui
13 Sa’an nan Solomon ya tafi Urushalima daga masujadar kan tudu a Gibeyon, da kuma daga gaban Tentin Sujada. Ya kuma yi mulki a bisa Isra’ila.
venit ergo Salomon ab excelso Gabaon in Hierusalem coram tabernaculo foederis et regnavit super Israhel
14 Solomon ya tara kekunan yaƙi da dawakai, ya kasance da kekunan yaƙi dubu da ɗari huɗu da kuma dawakai dubu goma sha biyu, waɗanda ya ajiye a biranen kekunan yaƙi, da kuma tare da shi a Urushalima.
congregavitque sibi currus et equites et facti sunt ei mille quadringenti currus et duodecim milia equitum et fecit eos esse in urbibus quadrigarum et cum rege in Hierusalem
15 Sarki ya sa azurfa da zinariya suka zama barkatai a Urushalima kamar duwatsu, al’ul kuma kamar itatuwan fir a gindin tsaunuka.
praebuitque rex argentum et aurum in Hierusalem quasi lapides et cedros quasi sycomoros quae nascuntur in campestribus multitudine magna
16 Aka shigo da dawakan Solomon daga Masar da kuma daga Kuye’yan kasuwan fada suka saye su daga Kuye.
adducebantur autem ei et equi de Aegypto et de Coa a negotiatoribus regis qui ibant et coemebant pretio
17 Suka shigo da kekunan yaƙi daga Masar a kan shekel ɗari shida-shida na azurfa, doki kuma a kan shekel ɗari da hamsin-hamsin. Suka kuma riƙa fitar da su ƙasashen waje zuwa dukan sarakunan Hittiyawa da na Arameyawa.
quadrigam equorum sescentis argenteis et equum centum quinquaginta similiter de universis regnis Cettheorum et a regibus Syriae emptio celebrabatur