< 2 Tarihi 2 >

1 Solomon ya ba da umarni don a gina haikali domin sunan Ubangiji da kuma fada wa kansa.
Now Solomon purposed to build a house for the name of the LORD, and a house for his kingdom.
2 Ya ɗebi mutane dubu saba’in su zama’yan ɗauko, mutane dubu tamanin su zama masu fasa dutse a tuddai, da kuma mutane dubu uku da ɗari shida su zama masu lura da su.
And Solomon counted out threescore and ten thousand men to bear burdens, and fourscore thousand men that were hewers in the mountains, and three thousand and six hundred to oversee them.
3 Solomon ya aika wannan saƙo ga Hiram sarkin Taya. “Ka aika mini gumaguman al’ul kamar yadda ka yi wa mahaifina Dawuda sa’ad da ka aika masa al’ul don yă gina fada yă zauna a ciki.
And Solomon sent to Huram the king of Tyre, saying: 'As thou didst deal with David my father, and didst send him cedars to build him a house to dwell therein, even so deal with me.
4 Yanzu ina shirin ginin haikali domin Sunan Ubangiji Allahna, in kuma keɓe shi gare shi don ƙona turare mai ƙanshi a gabansa, don kuma ajiyar burodi mai tsarki kullum, da kuma don miƙa hadayun ƙonawa kowace safiya, kowace yamma, da a Asabbatai da Sababbin Wata, da kuma a ƙayyadaddun bukukkuwan Ubangiji Allahnmu. Wannan dawwammamiyar farilla ce don Isra’ila.
Behold, I am about to build a house for the name of the LORD my God, to dedicate it to Him, and to burn before Him incense of sweet spices, and for the continual showbread, and for the burnt-offerings morning and evening, on the sabbaths, and on the new moons, and on the appointed seasons of the LORD our God. This is an ordinance for ever to Israel.
5 “Haikalin da zan gina zai zama mai girma, domin Allahnmu ya fi dukan sauran alloli girma.
And the house which I build is great; for great is our God above all gods.
6 Amma wa zai iya gina haikali dominsa, shi wanda sammai, har ma da sama sammai, ba za su iya riƙe shi ba? To, wane ne ni da zan gina haikali dominsa, in ba dai wurin ƙona hadayu a gabansa ba?
But who is able to build Him a house, seeing the heaven and the heaven of heavens cannot contain Him? who am I then, that I should build Him a house, save only to offer before Him?
7 “Saboda haka sai ka aiko mini da mutum wanda ya gwanince a aiki da azurfa, tagulla, baƙin ƙarfe, da kuma shunayya, da garura, da shuɗɗan zare, da wanda kuma ya gwanince da aikin sassaƙa, domin yă yi aiki tare da gwanayen mutane da nake da su a Yahuda da Urushalima, waɗanda mahaifina Dawuda ya tanada.
Now therefore send me a man skilful to work in gold, and in silver, and in brass, and in iron, and in purple, and crimson, and blue, and that hath skill to grave all manner of gravings, to be with the skilful men that are with me in Judah and in Jerusalem, whom David my father did provide.
8 “Ka kuma aika mini al’ul, fir da gumaguman algum daga Lebanon, gama na san cewa mutanenka sun gwanince a yakan katakai a can. Mutanena kuwa za su yi aiki tare da naka
Send me also cedar-trees, cypress-trees, and sandal-wood, out of Lebanon; for I know that thy servants have skill to cut timber in Lebanon; and, behold, my servants shall be with thy servants,
9 don su tanada mini katakai da yawa, domin haikalin da zan gina dole yă zama mai girma da kuma ƙasaitacce.
even to prepare me timber in abundance; for the house which I am about to build shall be great and wonderful.
10 Zan ba wa bayinka masu yankan katakai waɗanda suka yanka katako, garwa niƙaƙƙen alkama dubu ashirin, garwan sha’ir dubu ashirin da randunan ruwan inabi dubu ashirin da kuma randunan man zaitun dubu ashirin.”
And, behold, I will give to thy servants, the hewers that cut timber, twenty thousand measures of beaten wheat, and twenty thousand measures of barley, and twenty thousand baths of wine, and twenty thousand baths of oil.'
11 Hiram sarkin Taya ya amsa ta wurin rubuta wasiƙa zuwa ga Solomon. “Domin Ubangiji yana ƙaunar mutanensa, ya naɗa ka sarkinsu.”
Then Huram the king of Tyre answered in writing, which he sent to Solomon: 'Because the LORD loveth His people, He hath made thee king over them.'
12 Hiram ya ƙara da cewa, “Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya yi sama da ƙasa! Ya ba Sarki Dawuda ɗa mai hikima, cike da wayo da kuma sani, wanda zai gina haikali domin Ubangiji da kuma fada wa kansa.
Huram said moreover: 'Blessed be the LORD, the God of Israel, that made heaven and earth, who hath given to David the king a wise son, endued with discretion and understanding, that should build a house for the LORD, and a house for his kingdom.
13 “Zan aika maka Huram-Abi, wani gwani wanda ya iya aiki, kuma mai hikima,
And now I have sent a skilful man, endued with understanding, even Huram my master craftsman,
14 wanda mahaifiyarsa ta fito daga Dan, mahaifinsa kuma daga Taya. An horar da shi a aikin zinariya, azurfa, tagulla, baƙin ƙarfe, dutse, itace, da kuma shuɗi, shunayya, garura, da lilin mai kyau. Ya gogu a kowane irin zāne-zāne, zai kuma iya yin kowane zānen da aka ba shi. Zai yi aiki tare da masu sana’arka, da kuma tare da waɗanda ranka yă daɗe, Dawuda mahaifinka ya tanada.
the son of a woman of the daughters of Dan, and his father was a man of Tyre, skilful to work in gold, and in silver, in brass, in iron, in stone, and in timber, in purple, in blue, and in fine linen, and in crimson; also to grave any manner of graving, and to devise any device; to do whatever may be set before him, with thy skilful men, and with the skilful men of my lord David thy father.
15 “Yanzu fa, bari ranka yă daɗe, yă aiko wa bayinsa alkama da sha’ir da kuma man zaitun da ruwan inabin da ka alkawarta,
Now therefore the wheat and the barley, the oil and the wine, which my lord hath spoken of, let him send unto his servants;
16 za mu kuwa yanka dukan gumagumai daga Lebanon da kake bukata za mu kuwa yi fitonsu ta teku, su gangara zuwa Yaffa. Za ka iya kwashe su daga can ka haura zuwa Urushalima.”
and we will cut wood out of Lebanon, as much as thou shalt need; and we will bring it to thee in floats by sea to Joppa; and thou shalt carry it up to Jerusalem.'
17 Solomon ya ƙidaya dukan baƙin da suke cikin Isra’ila, bayan ƙidayan da mahaifinsa Dawuda ya yi; aka kuma tarar sun kai 153,600.
And Solomon numbered all the strangers that were in the land of Israel, after the numbering wherewith David his father had numbered them; and they were found a hundred and fifty thousand and three thousand and six hundred.
18 Ya sa 70,000 a cikinsu su zama’yan ɗauko, 80,000 kuma su zama masu fasan dutse a tuddai, sa’an nan 3,600 su zama shugabanni masu lura da aiki.
And he set threescore and ten thousand of them to bear burdens, and fourscore thousand to be hewers in the mountains, and three thousand and six hundred overseers to set the people at work.

< 2 Tarihi 2 >