< 1 Sama’ila 12 >

1 Sama’ila ya ce wa Isra’ilawa duka, “Na saurari abubuwan da kuka faɗa mini, na kuma naɗa muku sarki.
Then Samuel said to all of Israel, “I have paid attention to everything you asked from me, and I have given you a king to rule over you.
2 Yanzu kuna da sarki a matsayin shugaba, ni kuwa na tsufa har da furfura, yarana maza kuma suna tare da ku. Na yi shugabancinku tun ina yaro.
Now your king is your leader. I am old and gray, and my sons are here with you. I have led you from the time I was a boy up to today.
3 Ga ni a gabanku. Idan na yi wani abin da ba daidai ba sai ku faɗa a gaban Ubangiji, da gaban sarkin da ya keɓe. Ko na taɓa ƙwace saniya ko jakin wani? Ko na taɓa cuce wani, ko in danne hakkinsa? Ko na taɓa cin hanci daga hannun ɗayanku? Idan na taɓa yi ɗaya daga cikin waɗannan, sai ku faɗa mini, zan kuwa mayar masa.”
I stand here before you. Bring any charges you have against me in the presence of the Lord and of his anointed one. Have I taken anyone's ox or donkey? Have I wronged anyone? Have I oppressed anyone? Have I accepted a bribe from anyone to turn a blind eye? Tell me, and I will repay you.”
4 Suka ce, “Ba ka cuci ko danne hakkin kowa ba, ba ka ƙwace kome daga hannun kowa ba.”
“No, you have never cheated or oppressed us,” they replied, “and you have never taken anything from anyone.”
5 Sama’ila ya ce musu, “Ubangiji yă zama shaida a kanku, shafaffensa kuma yă zama shaida a wannan rana cewa ba ku same ni da wani laifin kome ba.” Suka ce, “I, shi ne shaida.”
Samuel told them, “The Lord is a witness, and his anointed is a witness today, in this case involving you, that you have not found me guilty of anything.” “He is a witness,” they replied.
6 Sa’an nan Sama’ila ya ce wa mutane, Ubangiji ne ya naɗa Musa da Haruna suka fitar da kakanninku daga Masar.
“The Lord is a witness, he who appointed Moses and Aaron,” Samuel went on. “He led your forefathers out of the land of Egypt.
7 Yanzu ku tsaya nan zan yi fito-na-fito da ku da shaida a gaban Ubangiji kan dukan ayyuka masu alherin da Ubangiji ya aikata saboda ku da kakanninku.
So stand here as I present to you in the presence of the Lord the evidence of all the good things the Lord has done for you and your forefathers.
8 Bayan da Yaƙub da’ya’yansa suka shiga Masar suka yi kukan neman taimako daga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya aika musu da Musa da Haruna. Su ne suka kawo kakanni-kakanninku daga Masar suka zauna a nan.
After Jacob had gone to Egypt, your fathers cried out to the Lord for help, and he sent Moses and Aaron to lead your forefathers out of Egypt and settle them here.
9 Amma suka manta da Ubangiji Allahnsu, shi kuma ya bashe su a hannun Sisera shugaban rundunar Hazor da kuma hannun Filistiyawa da sarkin Mowab wanda suka yi yaƙi da su.
But they forgot about the Lord their God, so he abandoned them to Sisera, the commander of the army of Hazor, to the Philistines, and to the king of Moab, who attacked them.
10 Suka yi kuka a gaban Ubangiji suka ce, “Mun yi zunubi mun bar Ubangiji, muka bauta wa Ba’al da Ashtarot. Amma ka cece mu yanzu daga hannun abokan gābanmu, mu kuwa za mu bauta maka.”
They cried out to the Lord for help and said, ‘We have sinned, for we have rejected the Lord and worshiped the Baals and Ashtoreths. Please save us from the hands of our enemies, and we will worship you.’
11 Sai Ubangiji ya aiki Yerub-Ba’al da Bedan da Yefta da Sama’ila, ya cece ku daga hannun abokan gābanku a kowane gefe domin ku sami cikakken zaman lafiya.
Then the Lord sent Gideon, Barak, Jephthah and Samuel, and he saved you from your enemies who surrounded you so you could live in safety.
12 Amma da kuka ga Nahash sarkin Ammonawa yana matsowa yă yaƙe, sai kuka ce mini, “Sam, muna so sarki yă shugabance mu.” Ko da yake Ubangiji Allahnku ne yake mulkinku.
But when you saw that Nahash, king of the Ammonites, was coming to attack you, you told me, ‘No, we want our own king,’ even though the Lord your God was your king.
13 Yanzu ga sarkinku da kuka zaɓa wanda kuka nema, ga shi Ubangiji ya naɗa muku sarki.
So here's the king you have chosen, the one you asked for. Look—the Lord now gives him to you as your king!
14 In kuka ji tsoron Ubangiji, kuka bauta masa, kuka yi masa biyayya, ba ku kuwa ƙi bin umarninsa ba, in kuma ku da sarkin da yake mulkinku kun bi Ubangiji Allahnku, to, za ku zauna lafiya.
If you honor the Lord, worship him, do what he tells you, and don't rebel against the Lord's instructions, and if both you and your king follow the Lord your God, then good!
15 Amma in ba ku yi biyayya ga Ubangiji ba, in kuma kuka ƙi bin umarnansa, fushinsa zai zauna a kanku.
However, if you refuse to do what he tells you, and rebel against the Lord's instructions, then the Lord will be against you as he was against your forefathers.
16 Yanzu ku tsaya tsit ku ga abin da Ubangiji ke dab da yi a gabanku.
Now stand still and watch what the Lord is going to do, right before your very eyes.
17 Ba lokacin yankan alkama ke nan ba? Zan roƙi Ubangiji yă aiko da tsawa da ruwan sama, za ku kuwa gane wace irin mugunta kuka yi a gaban Ubangiji sa’ad da kuka roƙa a ba ku sarki.
Isn't it the time of wheat harvest? Well, I will ask the Lord to send thunder and rain. Then you will realize how very evil you were in the Lord's sight when you demanded your own king.”
18 Sai Sama’ila ya roƙi Ubangiji, a ranar kuwa Ubangiji ya aiko da tsawa da ruwan sama. Dukan mutane suka ji tsoron Ubangiji da kuma Sama’ila.
Then Samuel prayed to the Lord, and that very day the Lord sent thunder and rain. Everyone was in absolute awe of the Lord and of Samuel.
19 Dukan mutane suka ce wa Sama’ila, “Ka yi addu’a ga Ubangiji Allahnka saboda bayinka, domin kada mu mutu, gama mun ƙara wa kanmu zunubi da muka roƙa a yi mana sarki.”
“Please pray to the Lord your God for us your servants, so we will not die!” they begged Samuel. “For we have added to all our sins the evil of asking for our own king.”
20 Sama’ila ya ce, “Kada ku ji tsoro.” Kun yi waɗannan mugunta duk da haka kada ku bar bin Ubangiji, amma ku bauta wa Ubangiji da dukan zuciyarku.
“Don't be afraid,” Samuel replied. “Even though you have indeed done all these evil things, don't give up following the Lord, but dedicate yourselves completely to worshiping him.
21 Kada ku bi alloli marasa amfani. Ba za su iya yi muku kome nagari ba, ba kuwa za su iya cece ku ba, gama ba su da amfani.
Don't worship worthless idols that can't help you or save you, for they are nothing.
22 Saboda suna mai girma da Ubangiji yake da shi, ba zai taɓa ƙin mutanensa ba. Gama Ubangiji ya ji daɗi da ya yi ku mutanensa.
The fact is because of the kind of person the Lord is, he won't give up on his people, because he was happy to claim you as his own.
23 Ni kam ba zai taɓa yiwu in yi wa Ubangiji zunubi ta wurin ƙin yin addu’a dominku ba. Zan koya muku hanyar da tana da kyau da ta kuma cancanta.
As for me, how could I sin against the Lord by no longer praying for you. I will also continue to teach you the way of goodness and right.
24 Amma ku amince za ku ji tsoron Ubangiji, ku bauta masa da aniya da dukan zuciyarku, kuna da manyan abubuwan da ya yi muku.
Make sure you honor God and worship him faithfully, with complete dedication. Think of all the tremendous things he has done for you.
25 Amma in kuka duƙufa cikin aikin mugunta da ku da sarkinku za a hallaka ku.
But if you continue to do what is evil, you and your king will be wiped out.”

< 1 Sama’ila 12 >