< 1 Bitrus 1 >
1 Bitrus, manzon Yesu Kiristi, Zuwa ga zaɓaɓɓu na Allah, baƙi a duniya, da suke a warwatse ko’ina a Fontus, Galatiya, Kaffadokiya, Asiya da kuma Bitiniya,
πετροσ αποστολοσ ιησου χριστου εκλεκτοισ παρεπιδημοισ διασπορασ ποντου γαλατιασ καππαδοκιασ ασιασ και βιθυνιασ
2 waɗanda aka zaɓa bisa ga rigyasanin Allah Uba, ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu, don biyayya ga Yesu Kiristi, su kuma sami yayyafan jininsa. Alheri da salama su zama naku a yalwace.
κατα προγνωσιν θεου πατροσ εν αγιασμω πνευματοσ εισ υπακοην και ραντισμον αιματοσ ιησου χριστου χαρισ υμιν και ειρηνη πληθυνθειη
3 Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi! Cikin jinƙansa mai girma ya ba mu sabuwar haihuwa cikin bege mai rai ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu,
ευλογητοσ ο θεοσ και πατηρ του κυριου ημων ιησου χριστου ο κατα το πολυ αυτου ελεοσ αναγεννησασ ημασ εισ ελπιδα ζωσαν δι αναστασεωσ ιησου χριστου εκ νεκρων
4 da kuma cikin gādon da ba zai taɓa lalacewa, ɓacewa ko koɗewa ba, ajiyayye a sama dominku,
εισ κληρονομιαν αφθαρτον και αμιαντον και αμαραντον τετηρημενην εν ουρανοισ εισ υμασ
5 ku waɗanda ta wurin bangaskiya ake kiyayewa ta wurin ikon Allah har yă zuwa ceton da yake a shirye da za a bayyana a ƙarshen lokaci.
τουσ εν δυναμει θεου φρουρουμενουσ δια πιστεωσ εισ σωτηριαν ετοιμην αποκαλυφθηναι εν καιρω εσχατω
6 A kan wannan kuke cike da farin ciki ƙwarai, ko da yake yanzu na ɗan lokaci kuna fuskantar baƙin ciki daga gwaje-gwaje iri-iri.
εν ω αγαλλιασθε ολιγον αρτι ει δεον εστιν λυπηθεντεσ εν ποικιλοισ πειρασμοισ
7 Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne, wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan gwada ta da wuta, domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi.
ινα το δοκιμιον υμων τησ πιστεωσ πολυ τιμιωτερον χρυσιου του απολλυμενου δια πυροσ δε δοκιμαζομενου ευρεθη εισ επαινον και τιμην και εισ δοξαν εν αποκαλυψει ιησου χριστου
8 Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa; kuma ko da yake ba kwa ganinsa yanzu, kun gaskata shi, kun kuma cika da farin ciki ƙwarai, wanda ya fi gaban faɗi,
ον ουκ ειδοτεσ αγαπατε εισ ον αρτι μη ορωντεσ πιστευοντεσ δε αγαλλιασθε χαρα ανεκλαλητω και δεδοξασμενη
9 gama kuna samun sakamakon bangaskiyarku, ceton rayukanku ke nan.
κομιζομενοι το τελοσ τησ πιστεωσ υμων σωτηριαν ψυχων
10 Game da ceton nan, annabawa, waɗanda suka yi maganar alherin da za tă zo gare ku, sun yi bincike mai zurfi, a natse,
περι ησ σωτηριασ εξεζητησαν και εξηρευνησαν προφηται οι περι τησ εισ υμασ χαριτοσ προφητευσαντεσ
11 suna ƙoƙari su san lokaci da kuma yanayin da Ruhun Kiristi da yake cikinsu yana nunawa sa’ad da ya yi faɗi a kan wahalolin Kiristi da kuma ɗaukaka da za tă bi.
ερευνωντεσ εισ τινα η ποιον καιρον εδηλου το εν αυτοισ πνευμα χριστου προμαρτυρομενον τα εισ χριστον παθηματα και τασ μετα ταυτα δοξασ
12 Aka bayyana musu cewa ba kansu ne suke bauta wa ba sai ku, sa’ad da suka yi maganar abubuwan da aka faɗa muku ta wurin waɗanda suka yi muku wa’azin bishara, ta wurin Ruhu Mai Tsarki wanda aka aika daga sama. Ko mala’iku ma suna marmari su ga waɗannan abubuwa.
οισ απεκαλυφθη οτι ουχ εαυτοισ υμιν δε διηκονουν αυτα α νυν ανηγγελη υμιν δια των ευαγγελισαμενων υμασ εν πνευματι αγιω αποσταλεντι απ ουρανου εισ α επιθυμουσιν αγγελοι παρακυψαι
13 Saboda haka, ku shirya kanku don aiki; ku zama masu kamunkai; ku kafa begenku duka a kan alherin da za a ba ku sa’ad da aka bayyana Yesu Kiristi.
διο αναζωσαμενοι τασ οσφυασ τησ διανοιασ υμων νηφοντεσ τελειωσ ελπισατε επι την φερομενην υμιν χαριν εν αποκαλυψει ιησου χριστου
14 Kamar’ya’ya masu biyayya, kada ku bi mugayen sha’awace-sha’awacen da dā kuke da su sa’ad da kuke rayuwa a cikin jahilci.
ωσ τεκνα υπακοησ μη συσχηματιζομενοι ταισ προτερον εν τη αγνοια υμων επιθυμιαισ
15 Amma kamar yadda wanda ya kira ku yake mai tsarki, haka ku ma sai ku kasance masu tsarki cikin dukan abubuwan da kuke yi;
αλλα κατα τον καλεσαντα υμασ αγιον και αυτοι αγιοι εν παση αναστροφη γενηθητε
16 gama a rubuce yake cewa, “Ku zama masu tsarki, domin ni mai tsarki ne.”
διοτι γεγραπται αγιοι γινεσθε οτι εγω αγιοσ ειμι
17 Tun da yake kuna kira ga Uba wanda yake yin wa kowane mutum shari’a bisa ga ayyukansa ba bambanci, sai ku yi rayuwarku a nan kamar baƙi cikin tsoro mai bangirma.
και ει πατερα επικαλεισθε τον απροσωποληπτωσ κρινοντα κατα το εκαστου εργον εν φοβω τον τησ παροικιασ υμων χρονον αναστραφητε
18 Gama kun san cewa ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa ko zinariya ce aka fanshe ku daga rayuwar banza da kuka karɓa daga kakanni-kakanninku ba,
ειδοτεσ οτι ου φθαρτοισ αργυριω η χρυσιω ελυτρωθητε εκ τησ ματαιασ υμων αναστροφησ πατροπαραδοτου
19 sai dai an fanshe ku da jini mai daraja na Kiristi, ɗan rago marar aibi ko lahani.
αλλα τιμιω αιματι ωσ αμνου αμωμου και ασπιλου χριστου
20 An zaɓe shi kafin halittar duniya, amma an bayyana shi a zamanin ƙarshe saboda ku.
προεγνωσμενου μεν προ καταβολησ κοσμου φανερωθεντοσ δε επ εσχατων των χρονων δι υμασ
21 Ta gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya tā da shi daga matattu, aka kuma ɗaukaka shi, ta haka bari bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.
τουσ δι αυτου πιστευοντασ εισ θεον τον εγειραντα αυτον εκ νεκρων και δοξαν αυτω δοντα ωστε την πιστιν υμων και ελπιδα ειναι εισ θεον
22 Yanzu da kuka tsarkake kanku ta wurin yin biyayya ga gaskiyan nan, don ku kasance da ƙauna mai gaskiya wa’yan’uwanku, sai ku ƙaunaci juna ƙwarai, daga zuciya.
τασ ψυχασ υμων ηγνικοτεσ εν τη υπακοη τησ αληθειασ δια πνευματοσ εισ φιλαδελφιαν ανυποκριτον εκ καθαρασ καρδιασ αλληλουσ αγαπησατε εκτενωσ
23 Gama an sāke haihuwarku, ba da iri da yake lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, ta wurin rayayyiya da kuma madawwamiyar maganar Allah. (aiōn )
αναγεγεννημενοι ουκ εκ σπορασ φθαρτησ αλλα αφθαρτου δια λογου ζωντοσ θεου και μενοντοσ εισ τον αιωνα (aiōn )
24 Gama, “Dukan mutane kamar ciyawa suke, darajarsu kuma kamar furannin jeji ne; ciyawa takan yanƙwane furannin kuma su kakkaɓe,
διοτι πασα σαρξ ωσ χορτοσ και πασα δοξα ανθρωπου ωσ ανθοσ χορτου εξηρανθη ο χορτοσ και το ανθοσ αυτου εξεπεσεν
25 amma maganar Ubangiji tana nan har abada.” Wannan kuwa ita ce kalmar da aka yi muku wa’azi. (aiōn )
το δε ρημα κυριου μενει εισ τον αιωνα τουτο δε εστιν το ρημα το ευαγγελισθεν εισ υμασ (aiōn )