< Actes 24 >

1 Cinq jours après, arriva le souverain sacrificateur Ananias avec les anciens et un avocat nommé Tertulle. Ils portèrent plainte au gouverneur contre Paul.
Bayan kwana biyar sai Ananiyas babban firist ya tafi Kaisariya tare da waɗansu daga cikin dattawa da kuma wani lauya mai suna Tertullus, suka kawo ƙararsu game da Bulus a gaban gwamna.
2 Celui-ci ayant été appelé, Tertulle se mit à l'accuser en ces termes:
Sa’ad da aka shigo da Bulus, sai Tertullus ya shiga kai ƙararsa a gaban Felis yana cewa, “Mun daɗe muna zaman lafiya a ƙarƙashinka, hangen nesanka kuma ya kawo gyare-gyare a wannan ƙasa.
3 «Très excellent Félix, nous reconnaissons en toute rencontre et en tout lieu, avec une entière gratitude, que c'est à toi et aux bonnes mesures que ta sollicitude t'a dictées pour cette nation, que nous devons la paix profonde dont nous jouissons.
Ko’ina da kuma a kowace hanya, ya mafifici Felis, mun amince da wannan da godiya marar iyaka.
4 Mais je ne veux pas t'arrêter plus longtemps, et je te prie de nous prêter, dans ta clémence, quelques moments d'attention.
Amma don kada in ƙara gajiyar da kai, ina roƙonka ka yi haƙuri ka saurari ɗan taƙaitaccen jawabinmu.
5 Le fait est qu'ayant trouvé cet homme, nous l'avons arrêté, parce que c'est une peste, un homme qui va semant la discorde parmi tous les Juifs répandus dans l'empire, un chef de la secte des Nazaréens;
“Mun tarar da wannan mutum fitinanne ne, yana tā-da-na-zaune-tsaye a tsakanin Yahudawa ko’ina a duniya. Shi shugaban ɗarikar Nazarawa
6 il a même tenté de profaner le temple. [Nous voulions le juger selon notre loi; ]
har ma ya yi ƙoƙari ya ƙazantar da haikali; shi ya sa muka kama shi.
7 [mais le tribun Lysias, étant survenu, l’a violemment arraché de nos mains, ]
8 [en donnant l’ordre à ses accusateurs de se rendre vers toi.] Tu pourras toi-même, en l'interrogeant, t’assurer par ses propres aveux, de tout ce que nous avançons à sa charge»
Ta wurin bincika shi da kanka za ka gane gaskiyar game da dukan waɗannan zargin da muke kawo a kansa.”
9 Les Juifs se joignirent à cette accusation, prétendant que c'était l’exacte vérité.
Yahudawa ma suka goyi bayan zargin, suna tabbatar cewa waɗannan abubuwa haka suke.
10 Mais Paul, à qui le gouverneur fit signe de parler, répondit: «C'est avec confiance que je prends la parole pour me justifier, sachant que depuis plusieurs années tu gouvernes cette nation.
Da gwamna ya yi masa alama yă yi magana, sai Bulus ya amsa ya ce, “Na san cewa ka yi shekaru da yawa kana mulki a wannan ƙasa; saboda haka ina farin ciki in kāre kaina.
11 Tu peux rassurer, qu'il n'y a pas plus de douze jours que je suis monté à Jérusalem pour adorer;
Da sauƙi za ka iya tabbatar cewa, bai fi kwana goma sha biyu da suka wuce ne na tafi Urushalima, domin yin sujada ba.
12 et l’on ne m'a vu parler à personne dans le temple, ni ameuter la foule, soit dans les synagogues, soit dans la ville.
Masu zargina ba su same ni ina gardama da kowa a haikali, ko kuma ina tā da hankalin jama’a a majami’u ko kuwa wani wuri dabam a cikin birni ba.
13 Ils ne peuvent pas trouver ce dont ils m'accusent maintenant.
Ba kuwa za su iya tabbatar maka ƙarar da suke yi yanzu a kaina ba.
14 Je te confesse que je sers le Dieu de mes pères selon la voie qu'ils appellent une secte, en croyant néanmoins toutes les choses qui sont écrites dans la Loi et dans les Prophètes,
Amma na yarda cewa ina bauta wa Allah na kakanninmu a matsayin mai bin Hanyar da suke kira ɗarika. Na gaskata dukan abin da ya amince da Doka da yake kuma a rubuce cikin Annabawa,
15 en ayant cette espérance en Dieu, comme ils l'ont eux-mêmes, qu'il y aura une résurrection tant des justes que des injustes:
ina kuma da irin bege ɗaya ga Allah yadda mutanen nan suke da shi, cewa akwai tashin matattu masu adalci da masu mugunta duka.
16 dans cette conviction, je m'efforce aussi moi-même d'avoir constamment une conscience irréprochable devant Dieu et devant les hommes.
Saboda haka, ina ƙoƙari kullum in kasance da lamiri mai tsabta a gaban Allah da mutane.
17 Après plusieurs années d’absence, je suis venu faire des aumônes à ma nation, et présenter des offrandes.
“Bayan’yan shekaru da dama da ba na nan, sai na dawo Urushalima don in kawo wa mutanena kyautai saboda matalauta in kuma yi sadaka.
18 C'est dans ces circonstances que des Juifs venus d'Asie m'ont trouvé, purifié, dans le temple, sans attroupement et sans tumulte.
Ni tsarkake ne sa’ad da suka same ni cikin filin haikalin ina yin haka. Babu taro tare da ni, ba kuwa ina tā da hankali ba.
19 C'était à eux de paraître en ta présence et de m'accuser, s'ils ont quelque plainte à porter contre moi;
Amma akwai waɗansu Yahudawa daga lardin Asiya, waɗanda ya kamata suna a nan a gabanka su kawo ƙara in suna da wani a kaina.
20 ou bien, que ceux-ci disent de quel crime ils m'ont trouvé coupable, lorsque j'ai paru devant le sanhédrin,
Ko kuwa waɗannan da suke a nan su faɗi laifin da suka same ni da shi sa’ad da na tsaya a gaban Majalisa,
21 à moins qu'ils ne me fassent un crime de cette seule parole, que j'ai prononcée lors de ma comparution devant eux: «C'est à cause de la résurrection des morts que vous me mettez aujourd'hui en jugement.»
sai ko wannan abu ɗaya kaɗai da na ɗaga murya na faɗi yayinda nake tsaye a gabansu cewa, ‘A game da tashin matattu ake mini shari’a a gabanku yau.’”
22 Mais Félix, qui connaissait assez bien ce qui se rapporte à cette croyance, les remit à un autre jour, disant: «Quand le tribun. Lysias sera venu, j'examinerai à fond votre affaire.»
Sai Felis, wanda yake da cikakken sani game da Hanyar, ya ɗaga sauraron ƙarar. Ya ce, “In Lisiyas shugaban ƙungiyar soja ya iso, zan yanke muku shari’a.”
23 Puis il commanda au centurion de tenir Paul en prison, d'avoir des égards pour lui, et de n'empêcher aucun des siens de lui rendre des services.
Ya yi wa jarumin umarni yă tsare Bulus amma yă ba shi’yanci yă kuma bar abokansa su lura da bukatunsa.
24 Quelques jours après, Félix étant venu avec Drusille sa femme, qui était Juive, fit chercher Paul et l'entendit sur la foi en Christ.
Bayan’yan kwanaki da dama sai Felis ya zo da matarsa Durusilla, mutuniyar Yahuda. Sai ya aika a zo da Bulus ya kuma saurare shi da yake magana game da bangaskiya cikin Kiristi Yesu.
25 Mais, comme Paul parlait de justice, de tempérance et de jugement à venir, Félix, effrayé, lui dit: «Pour le moment, va-t'en; à la première occasion, je te rappellerai.»
Da Bulus ya ci gaba jawabi a kan adalci, kamunkai da kuma hukunci mai zuwa, sai Felis ya tsorata ya ce, “Yanzu kam, ya isa haka! Kana iya tafi. In na sami zarafi, zan kira ka.”
26 Il espérait en même temps que Paul lui donnerait de l'argent: aussi le faisait-il venir assez fréquemment pour s'entretenir avec lui.
A wani fanni yana sa rai cewa Bulus zai ba shi toshiyar baki, saboda haka ya yi ta aika a kira masa Bulus yă yi magana da shi.
27 Deux ans s'étant écoulés, Félix eut pour successeur Porcius Festus, et, dans son désir de se rendre agréable aux Juifs, il laissa Paul en prison.
Da shekaru biyu suka wuce, sai Forsiyus Festus, ya gāji Felis, amma domin Felis ya so yă biya wa Yahudawa bukata, sai ya bar Bulus a kurkuku.

< Actes 24 >