< Ezra 8 >
1 And so these are the leaders of the families, with their genealogy, of those who ascended with me from Babylon, during the reign of king Artaxerxes.
Waɗannan su ne shugabannin iyalai, da kuma waɗanda suka dawo tare da ni daga Babilon a zamanin mulkin Sarki Artazerzes.
2 From the sons of Phinehas, Gershom. From the sons of Ithamar, Daniel. From the sons of David, Hattush.
Daga zuriyar Finehas, Gershom ne shugaba; daga zuriyar Itamar, Daniyel ne shugaba; daga zuriyar Dawuda, Hattush
3 From the sons of Shecaniah, the son of Parosh, Zechariah, and one hundred fifty men were numbered with him.
ɗan zuriyar Shekaniya ne shugaba, daga zuriyar Farosh, Zakariya ne shugaba, tare da shi akwai mutum 150;
4 From the sons of Pahath-moab, Eliehoenai, the son of Zerahiah, and two hundred men were with him.
daga Fahat-Mowab, Eliyehoyenai ɗan Zerahiya ne shugaba, tare da shi akwai mutum 200;
5 From the sons of Shecaniah, the son of Jahaziel, and three hundred men were with him.
daga zuriyar Zattu, Shekaniya ɗan Yahaziyel ne shugaba, tare da shi akwai mutum 300;
6 From the sons of Adin, Ebed, the son of Jonathan, and fifty men were with him.
daga zuriyar Adin, Ebed ɗan Yonatan ne shugaba, tare da shi akwai mutum 50;
7 From the sons of Elam, Jeshaiah, the son of Athaliah, and seventy men were with him.
daga zuriyar Elam, Yeshahiya ɗan Ataliya ne shugaba, tare da shi akwai mutum 70;
8 From the sons of Shephatiah, Zebadiah, the son of Michael, and eighty men were with him.
daga zuriyar Shefatiya, Zebadiya ɗan Mika’ilu ne shugaba, tare da shi akwai mutum 80;
9 From the sons of Joab, Obadiah, the son of Jehiel, and two hundred eighteen men were with him.
daga iyalin Yowab, Obadiya ɗan Yehiyel ne shugaba, tare da shi akwai mutum 218;
10 From the sons of Shelomith, the son of Josiphiah, and one hundred sixty men were with him.
daga Bani, Shelomit ɗan Yosifiya ne shugaba, tare da shi akwai mutum 160;
11 From the sons of Bebai, Zechariah, the son of Bebai, and twenty-eight men were with him.
daga Bebai, Zakariya ɗan Bebai ne shugaba, tare da shi akwai mutum 28;
12 From the sons of Azgad, Johanan, the son of Hakkatan, and one hundred and ten men were with him.
daga iyalin Azgad, Yohanan ɗan Hakkatan ne shugaba, tare da shi akwai mutum 110;
13 From the sons of Adonikam, who were the last, and these were their names: Eliphelet, and Jeuel, and Shemaiah, and sixty men were with them.
zuriya ta Adonikam ne suka zo daga ƙarshe, sunayensu kuwa su ne Elifelet, Yehiyel da Shemahiya, tare da su akwai mutum 60;
14 From the sons of Bigvai, Uthai and Zaccur, and seventy men were with them.
daga zuriyar Bigwai, Uttai da Zakkur ne shugabanni, tare da su akwai mutum 70.
15 Now I gathered them together at the river that runs down to Ahava, and we stayed there for three days. And I sought among the people and among the priests for the sons of Levi, and I found none there.
Na kuma tattara su a bakin rafi wanda yake gangarawa zuwa Ahawa, muka kafa sansani a can kwana uku. Da na bincika cikin mutane da firistoci, sai na tarar babu Lawiyawa.
16 And so I sent Eliezer, and Ariel, and Shemaiah, and Elnathan, and Jarib, and another Elnathan, and Nathan, and Zechariah, and Meshullam, who were leaders, and Joiarib and Elnathan, who were wise.
Saboda haka sai na aika a kira Eliyezer, da Ariyel, da Shemahiya, da Elnatan, da Yarib, da Natan, da Zakariya, da Meshullam waɗanda su ne shugabanni. Na kuma sa a kira Yohiyarib da Elnatan waɗanda masana ne.
17 And I sent them to Iddo, who is first within the place of Casiphia. And I placed in their mouth the words that they should speak to Iddo and his brothers, the temple servants, in the place of Casiphia, so that they would lead to us ministers for the house of our God.
Na sa su je wurin Iddo wanda yake shugaba a Kasifiya. Aka gaya musu abin da za su gaya wa Iddo da’yan’uwansa masu aiki a haikali a Kasifiya don su aiko mana waɗanda za su yi mana hidima a haikalin Allahnmu.
18 And because the good hand of our God was over us, they led to us a very learned man from the sons of Mahli, the son of Levi, the son of Israel, with Sherebiah, and his sons, and his eighteen brothers,
Da yake Allah yana tare da mu, sai suka aiko mana da Sherebiya, wanda ya iya aiki, shi daga zuriyar Mali ɗan Lawi ne, ɗan Isra’ila. Sai ya zo tare da’ya’yansa da kuma’yan’uwansa. Dukansu dai mutum 18 ne.
19 and Hashabiah, and with him Jeshaiah, of the sons of Merari, and his brothers, and his sons, numbering twenty.
Suka kuma aika da Hashabiya tare da Yeshahiya daga zuriyar Merari, da’yan’uwansu da kuma’ya’yansu, su kuma mutum 20 ne.
20 And from the temple servants, whom David, and the leaders had provided for the ministry of the Levites, there were two hundred twenty temple servants. All these were called by their names.
Sun kuma kawo masu aiki a haikali mutum 220, ƙungiyar da Dawuda da abokan aikinsa suka keɓe don su taimaki Lawiyawa aiki. Duk aka rubuta waɗannan da sunayensu.
21 And I proclaimed a fast in that place, beside the river Ahava, so that we might afflict ourselves in the sight of the Lord our God, and so that we might request of him the right way for us, and for our sons, and for all our substance.
A can, a bakin rafin Ahawa, na sa mu yi azumi, domin mu ƙasƙantar da kanmu a gaban Allah, mu kuma roƙe shi yă kiyaye mana hanya, da mu da’ya’yanmu da kayanmu duka.
22 For I was ashamed to petition the king for assistance and for horsemen, who would defend us from the enemy along the way. For we had said to the king: “The hand of our God is over all those who seek him in goodness. And his authority, and his strength and fury, is over all those who forsake him.”
Na ji kunya in roƙi sarki yă haɗa mu da sojoji da masu dawakai don su yi mana rakiya su kāre mu daga magabta a kan hanya, gama mun ce wa sarki, “Alherin Allah yana tare da duk wanda yake dogara gare shi, amma kuma fushinsa yana kan duk wanda ya juya masa baya.”
23 And so we fasted and begged our God for this; and as a result, we prospered.
Saboda haka sai muka yi azumi, muka kai roƙonmu a wurin Allah, ya kuwa amsa mana.
24 And I separated twelve from among the leaders of the priests: Sherebiah, and Hashabiah, and with them ten of their brothers.
Sai na keɓe manyan firistoci guda goma sha biyu tare da Sherebiya, Hashabiya da kuma’yan’uwansu guda goma.
25 And I weighed out to them the silver and the gold, and the vessels consecrated to the house of our God, which had been offered by the king, and by his counselors and his leaders, and by all those of Israel who had been found.
Na auna musu zinariya da azurfa, da kwanoni waɗanda sarki da mashawartansa, da sauran abokan aikinsa, da Isra’ilawan da suke can suka bayar domin haikalin Allahnmu.
26 And I weighed out to their hands six hundred fifty talents of silver, and one hundred vessels of silver, and one hundred talents of gold,
Na auna musu talenti 650 na azurfa, talenti ɗari na kwanonin azurfa, talenti 100 na zinariya,
27 and twenty gold bowls which had the weight of one thousand coins, and two vessels of the finest shining brass, as beautiful as gold.
kwanonin zinariya guda 20 da darajarsu ya kai darik 1,000, da kwanoni biyu na gogaggen tagulla, wanda yake darajarsa daidai da zinariya.
28 And I said to them: “You are the holy ones of the Lord, and the vessels are holy, with the silver and the gold, which has been offered freely to the Lord, the God of our fathers.
Na ce masa, “Ku da kayan nan tsarkaka ne ga Ubangiji. Azurfa da zinariya ɗin, bayarwa ce ta yardar rai ga Ubangiji, Allah na kakanninku.
29 Watch and guard them, until you weigh them out before the leaders of the priests and the Levites, and the rulers of the families of Israel in Jerusalem, into the treasury of the house of the Lord.”
Ku lura da su da kyau har sai kun isa Urushalima. Ku auna su a shirayin haikalin Ubangiji a Urushalima, a gaban manyan firistoci, da Lawiyawa, da shugabannin iyalai na Isra’ila.”
30 Then the priests and the Levites received the weight of the silver, and the gold, and the vessels, so that they might carry these to Jerusalem, into the house of our God.
Sa’an nan sai firistoci, da Lawiyawa suka karɓi azurfa da zinariya da kuma tsarkakan kwanonin da aka auna don a kai haikalin Allahnmu a Urushalima.
31 Therefore, we set out from the river Ahava, on the twelfth day of the first month, so that we might travel to Jerusalem. And the hand of our God was over us, and he freed us from the hand of the enemy and of those who lay in ambush along the way.
A rana ta goma sha biyu ga watan farko, muka tashi daga bakin rafin Ahawa don mu tafi Urushalima. Alherin Allahnmu yana tare da mu, ya kuma kāre mu daga magabta da’yan fashi.
32 And we arrived at Jerusalem, and we stayed there for three days.
Muka iso Urushalima, inda muka huta kwana uku.
33 Then, on the fourth day, the silver and the gold and the vessels were weighed out in the house of our God, by the hand of Meremoth, the son of Uriah, the priest; and with him was Eleazar, the son of Phinehas, and with them were the Levites, Jozabad, the son of Jeshua, and Noadiah, the son of Binnui.
A rana ta huɗu muka tafi haikalin Allah, muka auna azurfa, da zinariya, da tsarkakan kwanonin, muka ba Meremot ɗan Uriya firist, da Eleyazar ɗan Finehas yana tare da shi, da kuma Lawiyawan nan, wato, Yozabad ɗan Yeshuwa, da Nowadiya ɗan Binnuyi.
34 This was done according to the number and weight of everything; and every weight was written down at that time.
Aka yi lissafi aka auna kome aka tarar yana nan daidai, aka kuma rubuta yawan nauyin a lokacin.
35 Moreover, those who came from the captivity, the sons of the transmigration, offered holocausts to the God of Israel: twelve calves on behalf of all the people of Israel, ninety-six rams, seventy-seven lambs, and twelve he-goats for sin. All these were a holocaust to the Lord.
Sa’an nan sai waɗanda suka dawo daga bauta suka miƙa hadaya ta ƙonawa ga Allah na Isra’ila. Wato, bijimai guda goma sha biyu don Isra’ilawa duka, raguna tasa’in da shida,’yan raguna saba’in da bakwai, bunsurai kuma guda goma sha biyu. Aka miƙa su hadaya don zunubi. Wannan duka hadaya ta ƙonawa ce ga Ubangiji.
36 Then they gave the edicts of the king to the rulers who served in the sight of the king, and to the governors beyond the river, and they exalted the people and the house of God.
Suka kuma kai saƙon sarki zuwa ga wakilansa, da kuma gwamnoni na Kewayen Kogin Yuferites waɗanda suka taimaki mutane da kuma gidan Allah.