< Esajas 10 >

1 Ve dem, der giver Ulykkeslove og ivrigt fører Uret til Bogs
Kaiton waɗanda suke kafa dokokin rashin gaskiya, waɗanda suke ba da ƙa’idodin danniya,
2 for at trænge de ringe fra Retten og røve de armes Ret i mit Folk, at Enker kan blive deres Bytte og faderløse kan plyndres.
don su hana matalauta hakkinsu su kuma ƙi yin shari’ar gaskiya a kan waɗanda suke zaluntar mutanena, suna ƙwace wa gwauraye dukiyarsu suna kuma yi wa marayu ƙwace.
3 Hvad gør I paa Straffens Dag, naar Undergang kommer fra det fjerne? Til hvem vil I ty om Hjælp, hvor gemmer I da eders Rigdom?
Me za ku yi a ranan nan ta hukunci, sa’ad da masifa ta zo daga nesa? Ga wa za ku tafi don neman taimako? Ina za ku bar dukiyarku?
4 Enten maa I knæle blandt Fanger, eller ogsaa falde paa Valen! Men trods alt har hans Vrede ej lagt sig, hans Haand er fremdeles rakt ud.
Babu abin da zai rage sai cizon haƙora a cikin kamammu ko mutuwa cikin waɗanda aka kashe. Duk da haka, fushinsa bai huce ba, hannunsa har yanzu yana a miƙe.
5 Ve Assur, min Harmes Kæp, min Vrede er Stokken i hans Haand.
“Kaiton Assuriya, sandar fushina, a hannun da kulkin fushina yake!
6 Jeg sender ham mod et vanhelligt Folk, opbyder ham mod min Vredes Folk til at gøre Bytte og røve og trampe det ned som Skarn paa Gaden.
Na aike shi gāba da al’umma marar sanin Allah, na tura shi gāba da mutanen da suka ba ni fushi, don yă kwashe ganima yă kuma yi wason ganima, yă tattake su kamar laka a tituna.
7 Men han, han mener det ej saa, hans Hjerte tænker ej saa. Nej, at ødelægge, det er hans Attraa, at udrydde Folk, ikke faa.
Amma ba abin da ya yi niyya ke nan ba, ba abin da yake da shi a zuciya ba; manufarsa shi ne yă hallaka, yă kuma kawo ƙarshen al’ummai da yawa.
8 Thi han siger: »Er ej mine Høvedsmænd Konger til Hobe?
Ya ce, ‘Dukan shugabannin yaƙina ba sarakuna ba ne?’
9 Gik det ej Kalno som Karkemisj, mon ikke Hamat som Arpad, Samaria som Damaskus?
‘Kalno bai kasance kamar Karkemish ba? Hamat bai zama kamar Arfad Samariya kuma kamar Damaskus ba?
10 Som min Haand fandt hen til Afgudernes Riger, der dog havde flere Gudebilleder end Jerusalem og Samaria —
Yadda hannuna ya ƙwace mulkokin gumaka, mulkokin da siffofinsu suka fi na Urushalima da Samariya,
11 mon jeg da ikke skal handle med Jerusalem og dets Gudebilleder, som jeg handlede med Samaria og dets Afguder?«
ba zan yi da Urushalima da siffofinta yadda na yi da Samariya da gumakanta ba?’”
12 Men naar Herren fuldbyrder alt sit Værk paa Zions Bjerg og i Jerusalem, vil jeg hjemsøge Assyrerkongens Hjertes Hovmodsfrugt og hans Øjnes trodsige Pral,
Sa’ad da Ubangiji ya gama dukan aikinsa gāba da Dutsen Sihiyona da Urushalima, zai ce, “Zan hukunta sarkin Assuriya saboda fariya na gangancin zuciyarsa da kuma kallon reni na idanunsa.
13 fordi han siger: »Med min stærke Haand greb jeg ind, med min Visdom, thi jeg er klog. Jeg flyttede Folkeslags Grænser og rev deres Skatte til mig, stødte Folk fra Tronen i Almagt;
Gama ya ce, “‘Ta wurin ƙarfin hannuna ne na aikata wannan, da kuma ta wurin hikimata, gama ina da fahimi. Na kau da iyakokin ƙasashe, na washe dukiyarsu; a matsayina na mai iko, na mamaye sarakunansu.
14 min Haand fandt til Folkenes Rigdom som hen til en Fuglerede; som man sanker forladte Æg, har jeg sanket den vide Jord, og ingen rørte en Vinge, aabnede Næbbet og peb.«
Kamar yadda mutum yakan miƙa hannu cikin sheƙar tsuntsu haka hannuna ya je ya washe dukiyar al’ummai; kamar yadda mutane sukan tattara ƙwai, haka na tattara dukan ƙasashe; ba tsuntsun da ya kakkaɓe fikafiki, ko yă buɗe baki don yă yi kuka.’”
15 Mon Øksen bryster sig mod den, som hugger, gør Saven sig til mod den, som saver? Som om Kæppen kan svinge den, der løfter den, Stokken løfte, hvad ikke er Træ!
Gatari ya taɓa fin wanda yake amfani da shi girma, ko zarto yă yi wa wanda yake amfani da shi taƙama? Sanda za tă girgiza mutumin da yake riƙe da ita, ko kuwa kulki yă jijjiga mutumin da yake riƙe da katako!
16 Derfor sender Herren, Hærskarers HERRE, Svindsot i hans Fedme, og under hans Herlighed luer en Lue som luende Ild;
Saboda haka Ubangiji Maɗaukaki, zai aukar da cuta mai kisa a kan ƙosassu jarumawa; a ƙarƙashin sansaninsa zai ƙuna wuta kamar harshen wuta.
17 Israels Lys bliver til Ild og dets Hellige til en Flamme, og den brænder og fortærer hans Tidsel og Torn paa een Dag;
Hasken Isra’ila zai zo kamar wuta, Mai Tsarkinsu zai zama kamar wuta; a rana guda zai ƙone yă kuma cinye ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiyarsa.
18 hans Skovs og Frugthaves Herlighed skal den rydde Rub og Stub, og han bliver som en syg, der hentæres.
Darajar jejinsa da gonakinsa masu dausayi za a hallaka su ɗungum, kamar yadda ciwo yakan kashe mutum.
19 De Træer, som levnes i hans Skov, bliver det let at tælle; et Barn kan skrive dem op.
Sauran itatuwan jejinsa kuma za su ragu ko ɗan ƙaramin yaro ma zai iya ƙidaya su.
20 Paa hin Dag skal Israels Rest og det, som undslipper af Jakobs Hus, ikke mere støtte sig til den, der slaar det, men til HERREN, Israels Hellige, i Sandhed.
A wannan rana raguwar Isra’ila, waɗanda suka ragu na gidan Yaƙub, ba za su ƙara dogara ga wanda ya kusa hallaka su ba amma za su dogara ga Ubangiji, Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
21 En Rest skal omvende sig, Jakobs Rest, til den vældige Gud.
Raguwa za tă komo, raguwar Yaƙub za su komo ga Maɗaukaki Allah.
22 Thi var end dit Folk som Sandet ved Havet, Israel, kun en Rest deraf skal omvende sig. Ødelæggelse er fastslaaet, og med Retfærdighed vælter den frem;
Ko da yake mutanenka, ya Isra’ila, sun zama kamar yashin bakin teku, raguwa ce kurum za tă komo. A ƙaddara hallaka, mai mamayewa da mai adalci.
23 thi Ødelæggelse og fastslaaet Raad fuldbyrder Herren, Hærskarers HERRE, over al Jorden.
Ubangiji Maɗaukaki, zai sa hallakar da aka ƙaddara a kan dukan ƙasa ta faru.
24 Derfor, saa siger Herren, Hærskarers HERRE: Frygt ikke, mit Folk, som bor i Zion, for Assyrien, naar det slaar dig med Kæppen og løfter sin Stok imod dig som fordum Ægypten!
Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ya mutanena masu zama a Sihiyona, kada ku ji tsoron Assuriyawa, waɗanda suka dūke ku da sanda suka kuma ɗaga kulki a kanku, kamar yadda Masar ta yi.
25 Thi end om en føje Stund er Vreden ovre, og min Harme vender sig til deres Fordærv.
Ba da daɗewa ba fushina a kanku zai zo ga ƙarshe hasalata kuma za tă koma ga hallakarsu.”
26 Saa svinger Hærskarers HERRE Svøben imod det, som da Midjan blev slaaet ved Orebs Klippe; hans Stok er udrakt imod Havet, og han løfter den som fordum mod Ægypten.
Ubangiji Maɗaukaki zai bulale su da tsumagiya, kamar sa’ad da ya bugi Midiyan a dutsen Oreb; zai kuma ɗaga sandarsa a bisa ruwaye, yadda ya yi a Masar.
27 Paa hin Dag tager han Byrden af din Skulder og Aaget af din Nakke, ja, Aaget brister for Fedme.
A wannan rana zai ɗauke nauyi daga kafaɗarku, nauyinsu daga wuyanku; za a karye karkiya domin kun yi ƙiba ƙwarai.
28 Han rykker mod Ajjat, drager uden om Migron, i Mikmas lader han Trosset blive;
Sun shiga Ayiyat; sun bi ta Migron; sun adana tanade-tanade a Mikmash.
29 de gaar over Passet: »I Geba holder vi Natterast!« Rama ryster, Sauls Gibea flyr.
Suka ƙetare ta hanya, suka kuma ce, “Za mu kwana a Geba.” Rama ta firgita; Gibeya ta Shawulu ta gudu.
30 Skrig højt, Gallims Datter! Lyt til, Lajsja! Stem i, Anatot!
Ki yi ihu, ya Diyar Gallim! Ki saurara, ya Layisha! Kayya, Anatot abin tausayi!
31 Madmena flyr, Gebims Folk bjærger deres Gods.
Madmena tana gudu; mutanen Gebim sun ɓuya.
32 Endnu i Dag staar han i Nob; han svinger Haanden mod Zions Datters Bjerg, Jerusalems Høj —
A wannan rana za su dakata a Nob; za su jijjiga ƙarfinsu a dutsen Diyar Sihiyona, a tudun Urushalima.
33 Se, Herren, Hærskarers HERRE, afhugger hans Grene med Gru; de knejsende Stammer fældes, de stolte Træer maa segne.
Duba, Ubangiji Maɗaukaki, zai ragargaza rassa da iko mai girma. Za a sassare itatuwa masu ganyaye, za a yanke dogayen itatuwa har ƙasa.
34 Med Jernet gør han lyst i Skovens Tykning, og Libanon falder for den Herlige.
Zai sassare itatuwan jeji da gatari har ƙasa; Lebanon zai fāɗi a gaban Mai Iko.

< Esajas 10 >