< 2 Korinterne 4 >
1 Derfor, da vi have denne Tjeneste efter den Barmhjertighed, som er bleven os til Del, saa tabe vi ikke Modet;
Saboda haka, da yake ta wurin jinƙan Allah ne muke da wannan hidima, ba za mu fid da zuciya ba.
2 men vi have frasagt os de skammelige Smugveje, saa vi ikke vandre i Træskhed, ej heller forfalske Guds Ord, men ved Sandhedens Aabenbarelse anbefale os til alle Menneskers Samvittighed for Guds Aasyn.
Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafuncin da suke abubuwan kunya. Ba ruwanmu da ruɗu, ko yin ƙarya da kalmar Allah. Sai dai muna faɗin gaskiya a fili. Ta haka ne kowa zai yi shaidar gaskiyarmu a gaban Allah cikin zuciyarsa.
3 Men om ogsaa vort Evangelium er tildækket, da er det tildækket iblandt dem, som fortabes,
Ko da bishararmu a rufe take, tana a rufe ne ga waɗanda suke hallaka.
4 dem, i hvem denne Verdens Gud har forblindet de vantros Tanker, for at Lyset ikke skulde skinne fra Evangeliet om Kristi Herlighed, han, som er Guds Billede. (aiōn )
Allahn zamanin nan ya makanta hankulan marasa ba da gaskiya, yadda har ba za su iya ganin hasken bishara ta ɗaukakar Kiristi ba, wanda yake kamannin Allah. (aiōn )
5 Thi ikke os selv prædike vi, men Kristus Jesus som Herre, os derimod som eders Tjenere for Jesu Skyld.
Gama ba wa’azin kanmu muke yi ba, sai dai na Yesu Kiristi, a kan shi ne Ubangiji, mu kuma bayinku saboda Yesu.
6 Thi Gud, som sagde: „Af Mørke skal Lys skinne frem, ‟ han har ladet det skinne i vore Hjerter for at bringe Kundskaben om Guds Herlighed paa Kristi Aasyn for Lyset.
Domin shi Allah wanda ya ce, “Bari haske yă haskaka daga duhu,” ya sa haskensa ya haskaka a cikin zukatanmu, don yă ba mu hasken sanin ɗaukakar Allah a fuskar Kiristi.
7 Men denne Skat have vi i Lerkar, for at den overvættes Kraft maa være Guds, og ikke fra os,
Amma muna da wannan dukiya a cikin tulunan yumɓu, don a nuna wannan mafificin ikon nan daga Allah ne, ba daga gare mu ba.
8 vi, som trænges paa alle Maader, men ikke stænges inde, ere tvivlraadige, men ikke fortvivlede,
A matse muke a kowane gefe, sai dai ba a gurgunta mu ba. An rikitar da mu, amma ba mu fid da zuciya ba.
9 forfulgte, men ikke forladte, nedslagne, men ikke ihjelslagne,
An tsananta mana, amma ba a yashe mu ba, an fyaɗe mu da ƙasa, amma ba a hallaka mu ba.
10 altid bærende Jesu Dødelse om i Legemet, for at ogsaa Jesu Liv maa aabenbares i vort Legeme.
Kullum muna ɗauke da mutuwar Yesu a jikinmu, domin ran Yesu yă bayyana a jikinmu.
11 Thi altid overgives vi, som leve, til Død for Jesu Skyld, for at ogsaa Jesu Liv maa aabenbares i vort dødelige Kød.
Muddin muna a raye, kullum zaman mutuwa muke yi saboda Yesu, don a bayyana ran Yesu ta wurin jikin nan namu mai mutuwa.
12 Saaledes er Døden virksom i os, men Livet i eder!
Ta haka, mutuwa tana aiki a cikinmu, ku kuwa rai a cikinku.
13 Men efterdi vi have den samme Troens Aand, som der er skrevet: „Jeg troede, derfor talte jeg, ‟ saa tro ogsaa vi, og derfor tale vi ogsaa,
A rubuce yake cewa, “Na gaskata; saboda haka na yi magana.” Da wannan ruhun bangaskiya ne mu ma muka gaskata, saboda haka muke magana.
14 idet vi vide, at han, som oprejste den Herre Jesus, skal ogsaa oprejse os med Jesus og fremstille os tillige med eder.
Domin mun san cewa shi da ya tā da Ubangiji Yesu daga matattu, zai tashe mu mu ma tare da Kiristi, yă kuma miƙa mu a gabansa tare da ku.
15 Thi det sker alt sammen for eders Skyld, for at Naaden maa vokse ved at naa til flere, og til Guds Ære forøge Taksigelsen.
Duk wannan fa don amfaninku ne, domin alherin nan da yake bazuwa zuwa ga mutane masu yawa, yă zama dalilin godiya mai yawa ga ɗaukakar Allah.
16 Derfor tabe vi ikke Modet; men om ogsaa vort udvortes Menneske fortæres, fornyes dog vort indvortes Dag for Dag.
Saboda haka, ba mu fid da zuciya ba. Ko da yake a waje, jikinmu mai mutuwa yana lalacewa, amma can ciki, ana sabunta mu kowace rana.
17 Thi vor Trængsel, som er stakket og let, virker for os over al Maade og Maal en evig Vægt af Herlighed, (aiōnios )
Don wannan’yar wahalar tamu mai saurin wucewa, ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci. (aiōnios )
18 idet vi ikke se paa de synlige Ting, men paa de usynlige; thi de synlige ere timelige, men de usynlige ere evige. (aiōnios )
Domin ba abubuwan da ido yake gani ne muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa. Gama abubuwan da ake gani masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne. (aiōnios )