< 馬太福音 3 >

1 那時,洗者若翰出現在猶太曠野宣講說:
A waɗancan kwanaki, Yohanna Mai Baftisma ya zo, yana wa’azi a Hamadan Yahudiya
2 「你們悔改吧!因為天國臨近了。」
yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”
3 這人便是那藉先知依撒依亞所預言的:「在曠野有呼號者的聲音:你們該當預備上主的道路,修直衪的途徑。」
Wannan shi ne wanda aka yi maganarsa ta wurin annabi Ishaya cewa, “Ga murya mai kira a hamada tana cewa, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa.’”
4 這若翰穿著駱駝毛做的衣服,腰間束著皮帶,他的食物是蝗蟲和野蜜。
Tufafin Yohanna kuwa an yi su da gashin raƙumi ne, yana kuma daure da ɗamara ta fata. Abincinsa kuwa fāri ne da zumar jeji.
5 那時,耶路撒冷、全猶太以及全約但河一帶的人;都出來到衪那裏去,
Mutane suka zo wurinsa daga Urushalima da dukan Yahudiya da kuma dukan yankin Urdun.
6 承認自己的罪過,並在約但河裏受衪的洗。
Suna furta zunubansu, ya kuma yi musu baftisma a Kogin Urdun.
7 衪見到許多法利賽人和賽杜色人來受他的洗,就對他們說:「毒蛇的種類!誰指教你們逃避那即將來臨的忿怒﹖
Amma da Yohanna ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa suna zuwa inda yake yin baftisma, sai ya ce musu, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa fushin nan mai zuwa?
8 那麼,就結出與悔改相稱的果實吧!
Ku yi ayyukan da suka dace da tuba.
9 你們自己不要思念說:我們亞巴郎為父。我給你們說:天主能從這些石頭給亞巴郎興起子孫來。
Kada ma ku yi tunani a ranku cewa, ‘Ai, Ibrahim ne mahaifinmu.’ Ina gaya muku cewa Allah zai iya tā da’ya’ya wa Ibrahim daga cikin duwatsun nan.
10 斧子已放在樹根上了,凡不結好果子的樹,必被砍倒,投入火中。
An riga an sa bakin gatari a gindin itatuwa, kuma duk itacen da bai ba da’ya’ya masu kyau ba, za a sare shi a jefa cikin wuta.
11 我固然用水洗你們,為使你們悔改;但在我以後要來的那一位,比我更強,我連提衪的鞋也不配,衪要以聖神及火洗你們。
“Ina muku baftisma da ruwa domin tuba. Amma wani yana zuwa a bayana wanda ya fi ni iko, wanda ko takalmansa ma ban isa in ɗauka ba. Zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da kuma wuta.
12 衪的簸箕已在衪手中,衪要揚敬盡自己的禾場,將衪的麥粒收入倉內,至於糠秕,卻要用不滅的火焚燒。
Yana riƙe da matankaɗinsa, zai tankaɗe hatsinsa, yă kuma tattara alkamarsa a cikin rumbu, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.”
13 那時,耶穌由加里肋亞來到約但河若翰那裏,為受衪的洗;
Sai Yesu ya zo daga Galili, ya je Urdun don Yohanna yă yi masa baftisma.
14 但若翰想要阻止衪說:「我本來需要受你的洗,而你卻來就我嗎﹖
Amma Yohanna ya so yă hana shi, yana cewa, “Ina bukata ka yi mini baftisma, yaya kake zuwa wurina?”
15 耶穌回答衪說:「你暫且容許吧!因為我們應當這樣,以完成全義。」於是若翰就容許了衪。
Yesu ya amsa ya ce, “Bari yă zama haka yanzu; ya dace mu yi haka don mu cika dukan adalci.” Sa’an nan Yohanna ya yarda.
16 耶穌受洗後,立時從水裏上來,忽然天為他開了。他看見天主聖神有如鴿子降下,來到他上面;
Nan da nan da aka yi wa Yesu baftisma, sai ya fito daga ruwa. A wannan lokaci sama ya buɗe, sai ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya ya kuwa sauka a kansa.
17 又有聲音由天上說:「這是我的愛子,我所喜悅的」
Sai murya daga sama ta ce, “Wannan shi ne Ɗana wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai.”

< 馬太福音 3 >