< 路加福音 20 >
1 一天,耶穌在聖殿裏教訓百姓,及講喜訊的時候,司祭長、經師及長老前來,
Wata rana da Yesu yana koyar da mutane, yana musu wa’azin bishara a filin haikalin, sai manyan firistoci da malaman dokoki, tare da dattawan suka zo wurinsa.
2 對祂說道:「請你告訴我們:你憑什麼權柄作這些事﹖或者是誰給了你這權柄﹖」
Suka ce masa, “Gaya mana, da wane iko kake yin waɗannan abubuwa. Wa ya ba ka wannan ikon?”
3 耶穌回答他們說:「我也要問你們一句話,你們告訴我:
Ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Ku faɗa mini,
baftismar Yohanna, daga sama ne ta fito, ko kuwa daga wurin mutane ne?”
5 他們心裏忖度說:「如果我們說:是從天上來的,他必要說:你們為什麼不信他﹖
Sai suka yi shawara da junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai tambaya, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’
6 如果我們說:是從人來的,眾百姓必要用石頭砸死我們,因為他們都確信若翰是先知。」
Amma in kuma muka ce, ‘Daga mutane ne,’ dukan mutanen za su jajjefe mu da duwatsu, domin sun tabbata cewa, Yohanna annabi ne.”
Don haka, sai suka amsa cewa, “Ba mu san inda ta fito ba.”
8 耶穌也給他們說:「我也不告訴你們:我憑什麼權柄作這些事。」
Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku, ko da wane iko ne, nake yin waɗannan abubuwa ba.”
9 耶穌對百姓設了這個比喻:有一個人培植了一個葡萄園,把它租給園戶,就往遠方去,為時很久。
Sai ya ci gaba da gaya wa mutanen wannan misali ya ce, “Wani mutum ya yi gonar inabi, sai ya ba da hayarta ga waɗansu manoma, sa’an nan ya yi wata doguwar tafiya.
10 到了時節,他便打發一個僕人去園戶那裏,為叫他們把園中應納的果實交給他。園戶卻打了他,放他空手回去。
A lokacin girbi, sai ya aiki bawa zuwa wurin masu hayan, don su ba shi daga cikin’ya’yan inabin. Amma’yan hayan suka yi wa bawan nan dūka, suka kore shi hannu wofi.
11 園主又打發了另一個僕人去,他們把那人也打了,並加以侮辱,放他空手回去。
Ya sāke aikan wani bawa, shi ma suka yi masa dūka, suka kunyata shi, suka kuma kore shi hannu wofi.
12 園主又打發第三個去,連這一個,他們也打傷,把他趕了出去。
Har yanzu, ya sāke aikan na uku, amma suka ji masa rauni, suka jefar da shi waje.
13 葡萄園的主人說:我要怎樣辦呢﹖我要打發我的愛子去,或許他們會敬重他。
“Sai mai gonar inabin ya ce, ‘Me zan yi? Zan aiki ɗana da nake ƙauna, wataƙila za su girmama shi.’
14 誰佑園戶一看見,他便彼此商議說:這是承繼人,我們要殺掉,他好讓產業歸於我們。
“Amma da’yan hayan suka gan shi, sai suka tattauna zancen, suka ce, ‘Wannan shi ne magājin, mu kashe shi sa’an nan gādon zai zama namu!’
15 於是他們把他推到葡萄園外殺了。那麼,葡萄園的主人要怎樣處置他們呢﹖
Sai suka fitar da shi waje, suka kashe shi. “To, me mai gonar inabin zai yi da su?
16 他必要來,除滅這些園,戶把葡萄園租給別人。」眾人一聽這話,就說:「千萬不要這樣! 」
Zai zo ya karkashe masu hayan nan, ya ba wa waɗansu gonar inabin.” Da mutanen suka ji wannan, sai suka ce, “Allah ya sawwaƙa!”
17 耶穌注視他們說:「那麼,經上所載:『匠人棄而不用的石頭,反而成了屋角的基石,』這句話是什麼意思﹖
Yesu ya zura musu ido ya ce, “To, mene ne ma’anar abin da aka rubuta cewa, “‘Dutsen da magina suka ƙi, shi ne kuwa ya zama dutsen kan ginin’
18 凡跌在這石頭上的,必被撞碎;這石頭落在誰身上,必把他壓碎。」
Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Kuma in dutsen nan ya fāɗi a kan wani, zai murƙushe shi.”
19 經師及司祭長在那時刻就想下手逮捕耶穌,但是害怕百姓。他們明白這個比喻是暗指他們說的。
Malaman dokoki da manyan firistoci, suka nemi hanyar kama shi nan da nan, domin sun san cewa, ya yi wannan misali a kansu ne, amma suna jin tsoron mutane.
20 於是他們窺察耶穌,派遣奸細,假裝義人,要捉住他的語病,好把他交付於總督的司法權下。
Sai suka sa masa ido, suka aiki’yan leƙen asiri, waɗanda suka nuna kamar su masu gaskiya ne, suna nufin su kama shi game da abin da zai faɗa, domin su ba da shi ga gwamna mai mulki, da mai iko.
21 他們就詰問他說:「師傅,我們知道你說話施教,都正直無私;又不看情面,但按真理教授天主的道路。
Sai’yan leƙen asirin suka tambaye shi, suka ce, “Malam, mun sani kana faɗin, kuma kana koyar da abin da yake daidai, ba ka kuma nuna bambanci, amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya.
Daidai ne mu biya haraji ga Kaisar, ko babu?”
Ya gane makircinsu, sai ya ce musu,
24 「你們拿一個「德納」來給我看! 這「德納」上有誰的肖像,有誰的字號﹖」他們說:「凱撒的。」
“Nuna mini dinari. Hoton wane ne, kuma rubutun wane ne a kai?” Suka amsa, “Na Kaisar.”
25 耶穌對他們說:「那麼,凱撒的就應歸還凱撒;天主的,就應歸還天主。」
Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”
26 他們在民眾在面前,不能抓到祂的語病,且驚奇祂的應對,遂噤口不言。
Ba su iya kama shi a kan abin da ya faɗa a fili ba. Amsarsa ya ba su mamaki, shi ya sa suka yi shiru.
Waɗansu Sadukiyawa da suke cewa, ba tashin matattu, suka zo wurin Yesu da tambaya cewa,
28 「師傅,梅瑟給我們寫道:如果一個人的哥哥死了,撇下妻子而沒有子嗣,他的弟弟就應娶他的妻子,給他哥哥立嗣
“Malam, Musa ya rubuta mana cewa, ‘In ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata amma ba’ya’ya, dole mutumin ya aure gwauruwar, ya samo wa ɗan’uwansa’ya’ya.’
29 曾有兄弟七人,第一個娶了妻子,沒有子嗣就死了。
To, an yi waɗansu’yan’uwa bakwai. Na fari ya auri wata mace, ya mutu ba’ya’ya.
31 及第二個都娶過她為妻。七個人都是如此:沒有留下子嗣就死了。
da na ukun suka aure ta. Haka nan dukansu bakwai suka mutu babu’ya’ya.
A ƙarshe, ita macen ma ta mutu.
33 那麼,在復活的時候,這婦人是他們那一個的妻子﹖因為他們七個人都娶過她為妻。」
Shin, a tashin matattu, matar wa za tă zama? Tun da su bakwan nan, sun aure ta.”
34 耶穌對他們說:「今世之子也娶也嫁; (aiōn )
Yesu ya amsa ya ce, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna kuma ba da aure, (aiōn )
35 但那堪得來世,及堪當由死者中復活的人,也不娶也不嫁; (aiōn )
amma su waɗanda aka ga sun cancantar kasancewa a zamanin can, da kuma na tashin matattu, ba za su yi aure, ko su ba da aure ba. (aiōn )
36 甚至他們也不能再死,因為他們相似天使,他們既是復活之子,也就是天主之子。
Kuma ba za su sāke mutuwa ba, gama su kamar mala’iku ne. Su’ya’yan Allah ne, tun da su’ya’yan tashin matattu ne.
37 至論死者復活,梅瑟已在荊棘篇中指明了:祂稱為亞巴郎的天主,依撒格的天主及雅各伯的天主。
Amma bisa ga labari na bishiya nan, mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, ko Musa ma, ya nuna cewa, matattu suna tashi. Gama ya kira Ubangiji, ‘Allah na Ibrahim, da Allah na Ishaku, da kuma Allah na Yaƙub.’
38 祂不是死人的,而是活人的天主:所有人為祂都是生活的。」
Shi ba Allah na matattu ba ne, amma na masu rai ne, gama a gare shi, duka na da rai.”
Sai waɗansu malaman dokoki suka amsa suka ce, “Ka faɗi daidai, malam!”
Kuma ba wanda ya sami ƙarfin halin yin masa waɗansu tambayoyi.
41 耶穌問他們說:「人們怎麼稱默西亞達味之子呢。
Sai Yesu ya ce musu, “Yaya suke cewa, ‘Kiristi ɗan Dawuda ne?’
42 達味自己曾在聖詠集上說:『上主對吾主說:你坐在我右邊,
Dawuda da kansa ya faɗa a cikin Zabura, “‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana,
sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.”’
Dawuda ya kira shi ‘Ubangiji.’ Ta, yaya zai zama ɗansa?”
Yayinda dukan mutane suna cikin sauraronsa, sai Yesu ya ce wa almajiransa,
46 你們應慎防經師! 他們喜歡穿長袍遊行,喜愛街市上的致敬,會堂裏的高位,筵席上的首座。
“Ku yi hankali da malaman dokoki. Sukan so sa manyan riguna suna zaga, suna sha’awan karɓan gaisuwa a wuraren kasuwanci, da kuma wuraren zama mafi daraja a majami’u, da wuraren bangirma a bukukkuwa.
47 他們吞沒寡婦們的家產,而又以長久的祈禱作掩飾:這些人必要遭受更重的處罰。」
Suna mamaye gidajen gwauraye, kuma don burga, suna dogayen addu’o’i. Ga irin waɗannan mutane, za a yi musu hukunci mai tsanani sosai.”